✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

… Haka kuma tsohon kocin Najeriya ya rasu

A ranar Lahadin da ta wuce ne aka samu labarin rasuwar tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta kasa (Flying Eagles) Musa Abdullahi. Ya rasu ne…

A ranar Lahadin da ta wuce ne aka samu labarin rasuwar tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta kasa (Flying Eagles) Musa Abdullahi. Ya rasu ne a gidansa da ke Jihar Kogi yana da shekara 61 bayan ya yi fama da matsanancin rashin lafiya.

Kafar sadarwa ta Premiums Times ta binciko cewa tun cikin shekarar 2007 ne kocin ya kamu da cutar da ke shanye barayin jiki da aka fi sani da Stroke al’amarin da ya sa ba ya ya iya yin komai da kansa tun daga wancan lokaci har ya bar duniya.
Musa Abdullahi ya taba horar da kungiyar kwallon kafa ta kasa ta ’yan kasa da shekara 17 da aka fi sani da Golden Eaglets kafin daga bisani ya zama Kocin Flying Eagles daga nan kuma ya zama Mataimakin Kocin Super Eagles a lokuta daban-daban.
Manajan kulob din Kogi United Suleiman Ahmed ya tabbatar da mutuwar Musa Abdullahi a lokacin da aka tuntube shi.
Rahotanni sun tabbatar Musa Abdullahi ya rika neman taimakon Hukumar kula da wasanni ta kasa (National Sport Comission) da Hukumar Shirya Wasan kwallon kafa ta kasa (NFF) da sauran ’yan Najeriya amma hakan bai sa ya samu isassun kudin da suka sa ya samu kulawar da ta dace kafin rasuwarsa ba.