A yayin da alhazai ke shirin tsayuwar Arfa a ranar Litinin, samun damar gabatar da aikin Hajji a bana ya sanya alhazai zubar da hawayen farin ciki.
Wani dattijo mai shekara 58 wanda kuma ba dan Saudiyya ba ne, bai san lokacin da ya fashe da kuka ba bayan da aka zabe shi a cikin mutanen da za su gudanar da aikin Hajjin tare da iyalansa su biyar.
- Masu fasa-kwaurin shinkafa sun bude wa kwastam wuta
- Ya Jagoranci Kai Farmaki Kayukan Zamfara Saboda Kama Mahaifinsa
Amin wanda dan kasar Indiya ne mazaunin birnin Dammam na kasar Saudiyya daya ne daga cikin maniyyata 558,000 da suka nemi gurbin gudanar da ibadar da aka takaita ga mutum 60,000 a bana.
Farin cikin alhazai
Dattijon ya ce, “Muna cike da farin ciki duk da cewa akwai abokan arziki da danginmu da yawa da ba su samu dama ba”.
Shi ma wani dan asalin kasar Masar da ke zaune a Saudiyya, Mohammed El Eter, wanda aka zabe shi domin gabatar da ibadar a bana, ya ce ya rasa yadda zai bayyana farin cikinsa.
Matashin mai shekara 31 ya ce, “Wannan wani lokaci ne na musamman da ba za a iya mantawa da shi ba a rayuwar mutum. Na gode wa Allah da Ya ba ni wannan damar daga cikin dubun dubatar mutanen da suka nemi samun izini”.
“Abin da na ji ba za a iya kwatanta shi ba… kamar ka yi kuka… kusanci da Allah” inji wata mata ’yar kasar Syria mai suna Rania Azraq wacce za ta halarci aikin Hajji ba tare da muharrami ba.
Fifiko ga sabbin alhazai
A bana Ma’aikatar Aikin Hajjin da Umrah ta Saudiyya ta takaita ibadar ga mazauna kasarta daga kasashe 150 wadanda kuma suka kammala karbar allurar rigakafin COVID-19 wadanda shekarunsu ke tsakanin 18 zuwa 65 kuma ba sa tare da wata cuta mai tsanani.
Ta ce a wurin zaben alhazan bana, an bayar da fifiko ga mutanen da ba su taba sauke farali ba a ibadar ta kwana biyar da aka fara daga ranar Asabar.
Sai dai matakin da kasar ta sake dauka da nufin takaita yaduwar COVID-19 ta sanya kaduwa a zukatan miliyoyin maniyya a fadin duniya, baya ga caccaka ga gwamnatin kasar.
Matukar bakin ciki
Alhazan bana sun ninka mutum 10,000 wadada a shekarar 2020 suka sauke faralin ibadar da mutum sama da miliyan uku suka halarta a 2019.
Duk da haka maniyyatan da suka bukaci samun izinin ta manhajar tantancewar da kasar ta bullo da shi ta intanet a bana sun fusata matuka, inda suka ce zaman jiran da suka yi ta yi ya sa su cikin zullumi a kodayaushe.
Maniyyatan da ba su samu dama ba sun yi ta caccakar Ma’aikatar a kafafen sadar da zumunta.
Wani mai amfani da Twitter ya rubuta cewa, “Har yanzu muna cikin tsananin jiran a zabe mu, kamar wasu masu fuskantar jarrabawa.”
Wani dan kasuwa mai shekara 64 dan asalin kasar Pakistan mai suna Zafar Ullah ya ce, “Na yi matukar bakin ciki,” bayan Saudiyya ta sanar da hana maniyyata daga kasashen duniya.
Ya ce, “Ni ma na so zuwa aikin Hajji tun a bara kuma na yi matukar burin zuwa a bana kuma har ma na karbi allurar tare da matata.”
Ana son duk Musulmi mai hali ya yi aikin Hajji akalla sau daya a rayuwarsa.
A bara kasar Saudiyya ta ce mahajjata dubu daya ne kawai aka bai wa izinin yin ibadar, amma kafofin yada labarai na cikin gida sun ce mahajjata 10,000 ne suka halarta.
Tsadar aikin Hajji a COVID-19
Wasu daga cikin mahajjatan sun koka kan tsadar aikin ibadar wadda kudin da gwamnati ta kayyade yake farawa daga Riyal 12,100 ($3,226), baya ga karin harajin da aka yi.
A bara, mahajjata sun ce Masarautar ta dauki nauyin duk mahajjatan, inda ta ba su abinci, masauki da kuma kula da lafiyarsu.
Amma duk da tsadar, maniyyata sun ce kayyade yawan maniyyatan ya kara wa addini kima inda ake rige-rigen samun damar halarta.
Yayin da ake fama da cutar, mahajjata da yawa na ganin ya fi kyau a takaita yawan alhazai domin guje wa aukuwar abin da ake gudu na barkewar annoba.