Hukumar Kula da Harkokin Sufurin Jiragen Sama ta Kasar Saudiyya (GACA) ta amince da yi wa Najeriya karin wa’adin jigilar maniyyata domin aikin Hajjin bana har zuwa Laraba, kamar yadda Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta bukata.
Kafin karin wa’adin dai, ranar Litinin, hudu ga watan Yuli ce ranar cikar wa’adin da Saudiyya ta debar wa kasashen duniya domin jigilar maniyyatansu.
- Yadda aka gano badakalar N400m a Gwamnatin Zulum
- MURIC ta bukaci a dage jarabawar NECO ta ranar Babbar Sallah
Hakan ta faru ne kasancewar har zuwa yanzu mutum 27,359 ne kawai suka isa kasa mai tsarkin daga cikin adadin 43,008 da aka ba Najeriya yayin aikin na bana.
NAHCON dai ta bukaci karin wa’adin ne domin ta sami damar kwashe dukkan ragowar maniyyata sama da 15,000 din da ba a iya kashewa ba
Najeirya dai ta bukaci karin wa’adin ne sakamakon soke tashin jirage da dama da kuma tsaikon da aka samu yayin jigilar, saboda dalilai kamar na rashin samun kudaden guzuri, rashin kudaden biza da kuma rashin sakamakon gwajin cutar COVID-19.
Kafar yada labarai ta Hajj Reporters ta ce alkaluma na nuni da cewa a tsakanin 10 zuwa 13 ga watan Yuni kawai, an soke tashin jirage akalla guda tara saboda irin wadannan dalilan.
Sai dai NAHCON ta ce tana da kwarin gwiwar da wannan karin wa’adin, za ta kwashe dukkan maniyyatan da suka cika dukkan sharudan tafiya kafin lokacin.
Hukumar ta ce tuni daya daga cikin kamfanonin da ke jigilar na FlyNas ya amince ya rika amfani da manyan jiragensa guda hudu domin jigilar maniyyata 1,732 a kullum.