✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajjin Bana: NAHCON ta soma tantance kamfanonin da za su yi jigilar maniyyata

Shida daga cikin kamfanin bakwai na Najeriya ne

Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta fara tantancen kamfanonin jiragen saman da za su yi jigilar maniyyatan Najeriya zuwa kasa mai tsarki don Aikin Hajjin bana.

Akalla kamfanoni guda bakwai ne suka nuna sha’awarsu don yin aikin jigilar da suka hada da Azman Air da Med-View Airline da Max Air da FlyNas da Skypower Express da Westlink Airlines da kuma Arik Air.

Duka kamfanonin da lamarin ya shafa na Najeriya ne, in ban da kamfanin FlyNas da ya kasance daga Saudiyya.

Bayanai sun nuna shirin tantancewar zai maida hankali ne wajen duba bayanan da kamfanonin suka mika yayin hajjin 2020 biyo bayan kiran da NAHCON ta yi musu.

Majiyarmu ta ce da ma an riga an tantance kamfanonin kafin Hajjin 2020 wanda bai gudana ba sakamakon bullar annobar COVID-19.

Daya daga cikin kamfanonin ya shaida wa wakilinmu cewa, “Za a yi amfani da tsarin tantancewa na 2020 ne, abin da kawai aka bukaci mu yi shi ne sabunta bayananmu.”

Sai dai babu wani cikakken bayani a kan ko NAHCON za ta bi ka’idar nan da ta saba ta ba da kashi 50 na aikin jigilar ga kamfanonin jiragen saman Saudiyya, ka’idar da masu ruwa da tsaki a harkar sufurin jirgin sama a Najeriya suka nuna ba ta yi musu dadi.

Da aka nemi jin ta bakinta kan wannan batu, Kakakin NAHCON, Hajiya Fatima Sanda Usara ta tabbatar da lallai za a yi amfani da tsarin 2020 ne wajen tantance kamfanonin.

Ta kuma ce tuni an nada kwamitin da zai yi aikin tantance kamfanonin da lamarin ya shafa.