Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Yobe, Bukar Kime, ya ce an yi wa kusan duk maniyyata aikin Hajjin bana daga jihar allurar rigakafin COVID-19.
Ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da Aminiya ta wayar salula.
- An sauya shugaban tsaron Masallacin Harami bayan yunkurin kashe limami
- Mahajjata 60,000 za a bari su yi aikin Hajji a bana
Sannan ya ce an fara bita don wayar da kan maniyyatan duk da cewa har yanzu ba su samu cikakken bayani na yadda za a gudanar da aikin ibadar ba.
Dadin dadawa, ba a tabbatar wa kowace jiha da adadin kujerun da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta ware mata ba.
Sakataren ya ja hankalin maniyyata su tabbatar da kiyaye dokoki da ka’idoji da aka gindaya na kariya daga cutar ta COVID-19 musamman wajen yawaita wanke hannu da sanya takunkumi.