Allah cikin ikonSa da kudirarSa da izzarSa Ya nufe ni a bana na koma Hajji, bayan shafe shekara 19 cur, Allah bai nufa ba na koma ibadar da ke daya daga cikin shika-shikan Musulunci biyar ba. Kodayake a bara da bana Allah Ya nufa na je Umara a kasar Mai tsarki, inda Allah Ya kebe wasu wurare, kamar dakinSa Mai alfarma da ke birnin Makka da Muna da filin Arfa da Musdalifa da birnin Madina inda kabarin Annabin Rahama (SAW) da wadansu daga cikin sahabbansa suke da kuma cikin masallacinsa Mai alfarma da sauran muhimman masallatai da makabartu (ababen ziyara a cikin aikin ibadar). Dukan wadannan wuraren ibada da ziyara da na ambata da wadanda ban ambata ba, Allah cikin ikonSa Ya sa ba inda ake da su a duk fadin duniyar nan sai a waccan kasa. Kuma Allah Ya ce a niki gari a je can don ibadar aikin Hajji ko Umarah, amma fa Ya ce ga mai iko na lafiyar jiki da hanya da guzuri.
Sanin kowane Musulmi ne cewa aikin Hajji ya yi matukar shan bambam da aikin Umara. Yayin da ake iya yin Umara a kowane lokaci na shekara, kuma malamai suka ce mafi kyan lokacin yin Umara shi ne cikin watan Ramadan, amma Hajji Allah (SWT) Ya kebe lokacin yi a watannin Zul-kida da Zul-Hajji, sannan ko a cikin watannin akwai kwanaki musamman da aka ware a cikin watan Zul-Hijja don yin asalin aikin Hajji, kamar fita zuwa Muna da ake yi ranar 8 ga wata da zuwa filin Arfa don tsayuwar Arfar a ranar 9 da jifar jamrori da ake yi a ranakun 10 da 11 da 12 (har ma da 13 ga wanda ya so yin haka), da yin yanka na hadaya ga wanda ta kama da yin aski ko saisaye da sauran ayyuka. Ma’ana dai Aikin Hajji lokaci da wuri kebantattu yake da su, sabanin Umara da na ce za a iya yi a tsawon shekara. Sallah ta kullum-kullum ce, Zakka ma sau daya a shekara ake yi ga wanda ta hau kansa, azumin watan Ramadan na gari duka ne, wato ma’ana lokaci daya, Kalmar Shahada kuma da ita ake haihuwar kowane mutum, sai dai iyayensa su mayar da shi Yahudu ko Nasara, wato wanda ba Musulmi ba.
Alkawarin da Allah (SWT) Ya yi ga bayinSa da suka yi aikin Hajji ko Umara karbabbe na yafe musu zunubbansu ya sanya wanda duk ya yi imani da Allah da ManzonSa da Ranar Tashin kiyama, kuma yana da hali a cikin al’ummar Musulmi yake zuwa aikin Hajji da Allah Ya farlanta sau daya a rayuwa. Sauran da suka biyo baya kuma sunnah ne. A ra’ayina da kuma yadda na ji na wadansu, ba kasar da Musulmi zai je a duk duniya ya ji yana cikin natsuwa ta yin ibada, kuma ya ji an karbi ibadar, kamar kasar Saudiyya, amma fa ga wanda ya tsarkake niyyarsa, wajen yin ibadar don neman yardar Allah kuma ya yi kamar yadda Allah Ya ce. Malamai ma na kara mana da cewa wasu daga cikin alamomin maniyyaci ya dace an karbi Hajjinsa ita ce mutum ya daina aikata duk wata masha’a da alfasha da aka san yana yi, kafin tafiyarsa Hajjin. Allah Ka sa mun dace, amin summa amin.
Mai karatu bari in dawo kan kanun makalar tawa. Kamar yadda na ambata tun farko rabona da zuwa Hajji tun 1999, yau sama da shekara 19. Aikin Umrah kuwa tun a shekarar 2006, da na je sai a bara da bana da Allah Ya sa na koma. Tun wancan lokaci da na je aikin Hajji Allah Ya sa ni, nake ta begen ganin na koma, kasancewar na san lada da falalar da ke cikin Hajji ba kadan ba ne. To alhamdulillah wani attajiri da ya dauki nauyin Umarar bara da bana, shi ne dai ya sake daukar nauyin Hajjin nawa. Ina rokon Allah (SWT) Ya biya shi da mafificin alheri Ya duba bayansa kamar yadda Ya duba bayan magabatansa tare da ba shi jinkiri mai amfani Ya kuma karbi ransa cikin imani Ya tashe shi cikin imani gobe kiyama, amin summa amin.
Tun a bara a lokacin aikin Umara na fahimci cewa kasar Saudiyya ta himmatu wajen inganta da fadada Haramin Ka’aba, ko a bana da na koma na ga ayyukan sun ci gaba, bisa ga kokarin da mahukuntar kasar suke yi na ganin ana iya karbar masu ibada akalla miliyan takwas duk shekara. Wutar lantarki da hanyoyi kuwa ba a magana, inda duk na sa ni a Jiddah ko biranen Makka da Madina ko hanyar zuwa wadannan garuruwa ko hanyoyin zuwa Muna ko filin Arfa ko na Musdalifa wutar lantarki ce duk inda ka duba kamar rana. Allah Ya sa ni a cikin addu’o’ina sai da na rika hadawa da Allah Ya azurta kasarmu da wutar lantarki irin ta kasar Saudiyya da ba a daukewa daidai da dakika daya.
Bayan aikin fadada Ka’aba da ake kai na fahimci kuma Muna inda ka taka ta zama mai shimfide da kwalta. Kazalika na samu labarin cewa, tun bayan turmutsitsin wajen jifar Shaidan da aka samu a Hajjin shekarar 2015, aka fadada hanyoyi da wurin jifa sama da kasa, ta yadda duk irin yadda ka ga yawan mahajjata sun danno don yin jifar, isowa wurin ke da wuya za ka ga cewa ba yawan mutanen, kasancewar wurin ya wadata. A dai Munan, an shaida mini cewa a bana ne aka bullo da wasu kujeru da aka yi amfani da su a dakunan kwana. Wadannan kujeru an yi musu soson kujeru guda uku a jere, ta yadda in ka nade su za su koma cikin kujerar ka zauna, in kuma ka warware su sun zama katifar kwanciya don barci. Na’urorin sanyaya daki kuwa ba a magana, haka ban-dakuna, ni dai inda muka zauna babu cinkoso. Tsadar rayuwa da duniya ta shiga kuwa ka ce ta kai kasar ta Saudiyya, don kuwa duk wasu abubuwa irin su ruwan sha da lemo akasarin farashinsu sun tashi daga kan Riyal daya na kasar Saudiyya da wancan lokaci yake kwatankwacin Naira 5 zuwa 6, yanzu sukan kama daga Riyal 2 kwankwacin Naira 200, (Riyal 1 yanzu daidai yake da kusan Naira 100). Haka farashin shiga tasi ko bas duk sun daga, kada ka yi batun magani da ba ya tabuwa, idan ka ce za ka kwatanta shi da canjin Naira.
Babban abin da na ji dadi irin bullo da tsarin ciyar da mahajjata sau biyu a wuni, wannan yana taimakawa a tsarin kiwon lafiyarsu matuka. Amma kuma har yanzu akwai babbar matsala ta dole duk mahajjacin kasar nan ya tafi ta hannun hukuma sai ya share sama a kwana talatin kana zai dawo gida. Ina ta tambaya a kan haka amma na rasa amsa. Allah Ya maimata mana.