Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna, ta sanar da cewa, maniyyata za su iya fara biyan aƙalla Naira miliyan 8.4 a matsayin kuɗin aikin Hajjin 2025.
Hukumar ta kuma bayyana cewa an fara rijistar Hajjin 2025 a dukkanin ƙananan hukumomin 23 jihar.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Yunusa Mohammed Abdullahi ne, ya bayyana haka a wani shirin gidan rediyo a jihar.
Ya jaddada muhimmancin bin ƙa’idojin rijista a ƙananan hukumominsu.
Ya kuma bayyana cewa an samar da tsarin biyan kuɗin ne domin sauƙaƙa wa manoma.
Manoma za su biya aƙalla Naira miliyan 4.5 a matsayin ajiya, sannan su biya ragowar kuɗin bayan an girbe amfanin gona, amma cikin wa’adin da gwamnatin jihar ta ƙayyade.
Hukumar ta shawarci dukkanin masu niyyar zuwa aikin Hajjin su fara rijistarsu a kan lokaci kuma su bi ƙa’idojin da hukumar ta shimfiɗa.