✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajjin 2025: Kafin alƙalamin N8.5m maniyyata za su biya a Legas

Za su biya ne kafin Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da kuɗin kujerar Hajji

Maniyyatan aikin Hajjin shekarar 2025 za su fara sanya Naira miliyan 8.5 a Jihar Legas kafin a sanar da kuɗin kujera a hukumance.

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar ta sanar cewa maniyyatan da ke shirin sauke farali daga jihar za su fara biyan miliyan N8.5 ɗin ne  kafin Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa NAHCON ta ayyana kuɗin aikin Hajjin da ke tafe.

Shugaban hukumar jin daɗin alhazan ya ce maniyyata na iya tara miliyan 8.5 ɗin da kaɗan-kaɗan daga yanzu har zuwa lokacin da za a rufe biyan kuɗin.

A cewarsa, hakan zai ba sau damar yin tanadi domin cika burinsu na gudanar da aikin Hajji a Ƙasa Mai Tsarki cikin sauƙi.

Ya ƙara da cewa idan hukumar NAHCON ta sanya kuɗin kujerar aikin Hajji ƙasa da Naira miliyan 8.5 da maniyyata suka biya, za a mayar wa kowannensu rarar kuɗinsa.

Ya ba da tabbacin aiki tukuru domin sama wa alhazan jihar sauƙi a yayin aikin hajjin da ake tafe, ta hanyar sama musu masauki a kusa da harami a Makkah da Madina, da kuma lafiyayyen abinci iri-iri harbda na gida baya ba su kulawa yadda ta dace.