Gwamantin Tarayya ta bayyaan sunayen kamfanoni hudu da ta sahale wa aikin jigilar alhazan Najeriya a aikin Hajjin shekarar 2025 da ke tafe.
Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) farfesa Abdullah Usman ya sanar cewa an zabo kamfanonin ne daga cikin kamfanoni 11 da suka gabatar da bukatar a basu aikin jigialar alhazan.
Sanarwar da kakakin Hukumar NAHCON, Fatima Sanda Usara ta fitar ta ce kamfanonin da suka yi nasaa su ne Air Peace da Max Air da UMZa da kuma Fly-Nas na kasar Saudiyya.
Ta bayyana cewa kwamitin mutum 32 da ya tantance kamfanonin da suka yi aikin ya kunshi jami’an NAHCON da Hukumar Sufurin Jiragen Sama (NCAA) da Hukumar Filayen Jiragen Sama (FAAN) da Hukumar Hasashen Yanayi (NIMET) da Hukumar Sararin Samaniya (NAMA) da Hukumar Kyaye Haduran Jiragen Sama (NSIB) da Hukumar Kwastam da Hukuamr Yaki da Rashawa ta ICPC.
- Boko Haram sun kashe manoma 40, wasu sun ɓace a Borno
- Yadda muka kashe manyan yaran Bello Turji —Sojoji
- Aikin Naira tiriliyan 16 ya yi layar zana a kasafin 2025
Sauran sun hada da kwararru da a fannin ba da kwangila da shari’a da binciken kudade da sauransu.
Farfesa Abdullah Usman ya bayyana cewa Hukumar NAHCON da hukumomin Saudiyya sun riga sun rattaba hannu kan yarjejeniyar aikin Hajji da Umra na wannan shekara.
Ya sanaya hannu kan yarjejeniyar ne tare da mataimakin Ministan Hajji da Umrah, Dakta Abdulfatah Masahat, a birnin Jedda na kasar Saudiyya.