✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajji: Za mu cika alkawuran da muka yi wa alhazai –NAHCON

Ya ba da tabbacin gudanar da sahihin aiki.

Shugaban Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON), Zikrullah Hassan ya ba da tabbacin cewa hukumar za ta cika dukkan alkawuran da ta dauka na samar da ingantattun abubuwan bukata ga maniyyata a lokacin aikin hajjin 2023.

Hassan ya bayyana haka ne yayin bankwana da tawagarta farko a Abuja, kafin tashinsu zuwa Kasa Mai Tsarki a ranar Asabar.

Ya bayyana cewa rikicin da Sudan ke haifarwa ba zai hana fara jigilar maniyyatan Najeriya a ranar Alhamis 25 ga watan Mayu ba.

A cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan yada labarai na NAHCON, Mousa Ubandanwaki ya fitar, shugaban ya yi addu’ar Allah Ya taimaki hukumar wajen gudanar da aikin Hajjin bana.

Ya kuma bukaci tawagar da ta kunshi jami’an NAHCON 31 da su tsara tare da daidaita masauki, ciyarwa da sufuri, kula da lafiya da jin dadin alhazai a kasa mai Tsarki a duk tsawon lokacin aikin Hajji.

“Dole ne ku kasance masu himma, jajircewa, taka tsan-tsan, hakuri da yin aiki yadda ya kamata a kowane lokaci, ta yadda a karshe za ku iya cimma moriyar duniya da lahira,” in ji shi.

Ya kuma bayyana aikin Hajji a matsayin wani lamari da ya shafi duniya baki daya, wanda manufarsa ita ce samar da hadin kai a tsakanin al’ummar Musulmi.

Don hkaka ya shawarci jami’an da su dauki aikinsu da muhimmanci ta hanyar zayyana kyawawan manufofi da hanyoyin samun nasara a ayyukansu.