✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajji: Yau za mu kammala kwashe maniyyata — NAHCON 

NAHCON ta ce a ranar 22 ga watan Yuni, za ta fara jigilar alhazai domin dawowa gida Najeriya.

Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ta ce a ranar Litinin za ta kammala kwashe maniyyata zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin bana.

Wannan na zuwa ne bayan da hukumomin Saudiyya suka sanar da lokacin rufe filin jirgin Sarki Abdul’aziz da ke Jeddah.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X (Twitter), mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar, Fatima Sanda Usara, ta ce “Jirgin ƙarshe na maniyyata zuwa aikin Hajjin 2024 zai tashi daga Abuja da safiyar ranar Litinin, 10 ga watan Yuni, 2024, inda zai nufi Madina.”

Ana dai sa ran cewa jirgin zai ɗauki kimanin alhazai 211 daga Zamfara, Sakkwato, Kebbi, Bauchi, Abuja da kuma Jihar Neja, tare da rukunin ƙarshe na jami’an NAHCON a cikin jirgin FlyNas.

Hakan ne ya kawo ƙarshen “jigilar alhazai na bana zuwa ƙasa mai tsarki, inda Aero Contractors za su kammala jigilar alhazai masu zaman kansu da ƙarfe 2:00 na rana a yau (Litinin),” in ji hukumar.

Ana kuma sa ran kamfanin Aero Contractors masu jigilar maniyyata masu zaman kansu, su kammala jigilar maniyyatan da ƙarfe 2 na ranar Litinin, kafin rufe filin jirgin saman Jeddah da Madina don gudanar da ayyukan jigilar alhazai masu shigowa.

NAHCON, ta ce a ranar 22 ga Yuni, 2024, ta ke shirya fara jigilar alhazanta zuwa Najeriya bisa tsarin waɗanda suka fara shiga su ne za su fara komawa.