✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajji: Gwamnatin Kano ta kafa cibiyar lafiya a Makkah

Kano ce kaɗai jihar da NAHCON ta amincewa kafa cibiyar lafiya ga maniyyanta.

Gwamnatin Jihar Kano, ta kafa ɗakunan shan magani ga mahajjata a garin Makkah, da ke ƙasar Saudiyya.

Aminiya ta ruwaito cewa aƙalla mahajjata 3110 ne, daga jihar za su yi aikin hajjin bana a ƙasa mai tsarki.

Cibiyar, a cewar shugaban tawagar yaɗa labaran mahajjata Kano, Ibrahim Garba Shu’aibu, na da nufin ƙara bin tsarin Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON).

“Jami’an NAHCON sun ziyarci wajen kuma sun amince da cibiyar da ta fara aiki,” in ji shi.

Ya sanar da cewa Kano ce kaɗai jihar da NAHCON ta amince ta buɗe cibiyar lafiya ga maniyyanta a Makkah.

Maniyyatan za su shafe kwanaki a Makka suna gudanar da ibada da ta haɗa da ɗawafi a Ka’aba, da yin sallah a babban masallaci da kuma yin hadayar dabbobi.

Aikin Hajji na ɗaya daga cikin rukunnan Musulunci guda biyar kuma ya wajabta ga duk wani Musulmi da ke hankali, yake kuma da iko.