✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hajji: An fara dawo wa maniyyata kudadensu a Kaduna

An fara rabawa wanda suke son karbar kudadensu.

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna ta fara mayar wa maniyyata 620 da suka nuna sha’awar karbar kudadensu bayan soke aikin Hajji a bana.

Shugabar hukumar, Hajiya Hannatu Zailani, ta bayyana hakan ne a yayin da ta fara ba da cakin kudi ga maniyyatan da suke bukatar kudaden nasu.

Hajiya Hannatu ta ce daga cikin maniyyata aikin Hajji 3,938 na 2021 a Jihar mutum 620 sun bukaci a dawo musu da kudadensu.

A cewarta, mayar da kudaden ga maniyyatan ya biyo bayan soke aikin Hajji da gwamnatin kasar Saudiyya ta yi saboda cutar COVID-19.

Ta ce Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON), ta ba bukaci maniyyatan da suke son karbar kudadensu da su koma jihohinsu don karbar kudaden.

“Mutum 620 sun nuna sha’awar karbar kudadensu kuma mun sanar da gwamnatin Kaduna.

“Wadanda suke son karbar kudadensu sai su karbi cakinsu yadda aka tsara sannan su bi matakan kariyar COVID-19,” a cewarta.

Ta ce za a biya kudaden rukuni-rukuni, wanda za a fara da shiyyar A, B da kuma C.