✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajji 2022: Ranar Alhamis za a fara jigilar alhazan Najeriya

Jami'an Hukumar Aikin Hajji ta kasa za su bar Najeriya zuwa Saudiyya ranar 6 ga watan Yuni domin tarbar alhazai ranar 9 ga wata

Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta sanar da ranar Alhamis 9 ga watan Yuni, 2022 a matsayin ranar da za a fara jigilar alhazai daga Najeriya zuwa Kasa Mai Tsarki.

Shugaban Hukumar NAHCON, Hassan Zikrullah ne ya sanar da hakan a lokacin taron sanya hannu kan yarjejeniyar jigilar alhazan tsakanin hukumar da kamfanonin jiragen sama da aka bai wa aikin, ranar Juma’a a Abuja.

Ya ce Hukumarsa ta tura wa Hukumar Aikin Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya bukatar karin kujerun aikin Hajji ga Najeriya, kuma hukumar tasa tana jiran amsa.

Ya bayyana cewa rukunin farko ta jami’an hukumarsa za su bar Najeriya zuwa kasar Saudiyya a ranar Litinin 6 ga watan Yuni, domin tarbar alhazai daga ranar Alhamis 9 ga watan Yuni.

A cewarsa, an sanyar 9 ga watan Yuni domin fara jigilar ce domin bayar da isasshen lokacin kammala shirye-shiryen jigilar maniyyata daga Najeriya.

Kamfanonin jigilar alhazai

Zikrullah ya bayyana cewa kamfanonin jiragen sama uku ne Hukumar ta sahale wa jigilar alhazai daga Najeriya a bana — MaxAir, Azman Air da kuma FlyNas.

Don haka ya bukaci kamfanonin da su bai wa alhazai kulawa ta musamman a matsayinsu na bakin alfarma.

Alhaji Zikrullah ya bayyana cewa an zabi Azman Air da MaxAir da Flynas ne daga cikin kamfanonin jiragen sama bakwai da suka nemi a ba su aikin jigilar alhazan.

“Azman Air da MaxAir kamfanonin cikin gida ne, FlyNas kuma daga kasar Saudiyya, bisa sharadin rabon jigilar alhazai tsakanin kasashe masu alhazai da kuma kasar Saudiyya.

“Kamfanoni bakwai da suka nemi a ba su aikin jigilar su ne MaxAir, FlyNas, Azman Air, Med-View Airline, Skypower Express, Westlink Airlines da kuma Arik Air.

“Guda ukun da suke kan gaban ne aka mika wa Fadar Shugaban Kasa sunayensu, ta ba su aikin,” inji Shugaban na NAHCON.

Jihohin da jiragen za su kwashi alhazansu

Jihohi 13 ne Max Air zai yi jigilar alhazansu da suka hada da Adamawa, Bauchi, Binuwai, Borno, Gombe da Jigawa.

Sauran su ne jihoihn Katsina, Kogi, Kwara, Nasarawa, Neja, Filato da kuma Jihar Taraba.

Azman Air kuma an ba shi jigilar alhazan jihohi 16 da kuma sojoji.

Jihohin su ne: “Kano, Abia, Akwa Ibom, Anambra, Bayelsa, Kuros Riba, Delta, Ebonyi da Ekiti.

Sauran su ne jihohin Enugu, Imo, Kaduna, Ogun, Ondo, Ribas, da Yobe.

Shi kuma FlyNas zai dauki alhazai daga jihohihin Edo, Abuja, Legass, Osun, Oyo, Sakkwato, Kebbi, da kuma Zamfara- wato jihohi takwas.”

Da yake nasa jawabin, Kwamishinan Ayyuka na Hukumar NAHCON, Abdullahi Magaji Hardawa, ya taya kamfanonin jiragen da suka samu aikin murna.

Sannan ya shawarce su da su yi aiki tukuru, ganin cewa rabon da a je aikin Hajji daga Najeriya tun shekara 2019, saboda bullar cutar COVID-19.