Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta umarci hukumomin kula da jin dadin alhazai na jihohi da su fara shirye-shiryen aikin Hajjin 2022.
Shugaban Hukumar NAHCON, Zikrullah Kunle Hassan, ya bayar da umarnin ne bayan samun sako daga mahukuntan kasar Saudiyya game da fara shirye-shiryen gudanar da aikin hajjin na 2022.
- An kashe ’yan bindiga sama da 200 a kwana 4 a Neja
- NAJERIYA A YAU: Wahalar Fetur A Najeriya: Da Sauran Rina A Kaba
Jami’ar Hulda da Jama’a ta NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta tabbatar wa wakilinmu cewa Shugaban Hukumar ya bayar da umarnin ne bayan zaman da hukumarsa ta yi da shugabannin huumokin kula da jin dadin alhazai na jihohi daga fadin Najeriya a ranar Laraba.
Zikrillah, ya bayyana wa taron cewa a wannan karon, Ma’aikatar Kula da Aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya ce kadai za ta tsara shirye-shiryen kafin fara aikin Hajjin, sabanin yadda a baya ake yin shirye-shiryen tare da hukumomin alhazan sauran kasashe.
Don haka ya umarci hukumomin jin dadin alhazai na jihohi da su mayar da duk kudaden da maniyyata suka biya a karkashin tsarin adashin gata zuwa asusun da hukumar ta ware a Bankin Jaiz, domin tafiyar da tsare-tsaren a bai-daya a bana.
Shekara biyu ke nan yanzu hukumomin Saudiyya ba su sahale wa baki da ’yan kasar mazauna wasu kasashe zuwa su sauke farali ba, tun bayan bullar annobar coronavirus a karshen shekarar 2019.
Bullar cutar a sassan duniya ta sa aka rufe makarantu da masallatai da kasuwanni da sauran wuraren taruwar jama’a, ciki har da Masallacin Harami.
A shekarar 2020 mutum 10,000, mazauna Saudiyya kacal ne Hukumar Kula da Aikin Hajji da Umrah ta Masarautar Saudiyya ta ba wa izinin gudanar da aikin Hajji cikin tsauraran matakan kariyar coronavirus.
A 2021 kuma, bayan sassauta wasu dokokin kariyar cutar coronavirus, hukumomin Saudiyya suka kara yawan mahajjata zuwa mutum 60,000 wadanda dukkannin suna zaune ne a kasar.
Duk da haka, ba a amince mahajjata su taba dakin Ka’aba ba, haka kuma ba a yarda wadanda ba mahajja ba ne su shiga Mataf, wato harabar Ka’aba, domin yin dawafi, da dai sauran matakai.
Bayan haka ne dai hukumomin Saudiyya suka sassauta wasu dokokin kariyar coronavirus a kasar, ciki har da bude masallatan cikin unguwanni tare da kara yawan masu shiga masallatan Harami da dai sauransu.