Kasar Saudiyya ta yi nisa da aikin sanya alamu a zagayen dakin Ka’abah domin tabbatar da bayar da tazara tsakanin Mahajjata a lokacin dawafi domin hana yaduwar cutar coronavirus.
Zuwa yanzu an lika wa daben da ke zagaye da Ka’abah alamomi masu launuka daban-daban da ke nuna inda masu dawafi za su rika bi da kuma inda za su bari babu kowa.
Ana kuma yin feshin magani akai-akai a fadin Masallacin Haramin da sauran wuraren da suka danganci ibadar, wadda annobar ta tilasta rage yawan mahalartanta daga sama da miliyan daya zuwa mutum 10,000.
Lamarin cutar ya sa Saudiyya kara yawan harsunan da za a fassara hudubar ranar Arfah zuwa guda 10 ciki har da harshen Hausa.
Fassarar hudubar zuwa harsunan za su kasance ne kai tsaye, a yayin da limamin ke gabatarwa da harshen Larabci a Masallacin Namira da ke Arfa, inda alhazai ke yin sallolin Azahar da La’asar.
An kuma tanadi kofofi masu feshin maganin kashe kwayar cuta domin duk masu shiga wuraren aikin Hajji (Masha’ir).
Kazalika an sanya alamun bayar ta tazara a tsakanin sahun sallah da sauran wurare a masallatan da alhazai ke amfani da su a Makkah da Muzdalifa, inda Mahajjata za su kwana ranar Arfa.
Ana kuma ci gaba da yi wa alhazai da ke isa Makkah daga sassan kasar gwaji domin tabbatar da ba su dauke da cutar.
Alhazan na ci gaba da sauka a masaukansu na Makkah inda za su kasance a killace har zuwa ranar takwas ga watan Zhul Hajji, kafin su wuce zuwa Mina.
Za a rika yi musu gwajin cutar a kowace rana daga isarsu har zuwa karshen aikin Hajji.
Kazalika Hukumar Aikin Hajji da Umarah da Ma’aikatar Lafiya ta Kasar Saudiyya sun da dauki kwararan matakan hana yaduwar cutar a kowace gaba ta aikin Hajjin.