A yayin da shirye-shirye suka kanakama na fara jigilar maniyyata aikin Hajjin shekarar 2022 ranar Alhamis, maniyya 1,105 ne za su sauke farali daga Jihar Gombe.
Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai na jihar, Sa’adu Hassan, ne ya bayyana hakan a lokacin taron da ya gudanar da ma’aikatan hukumar, inda ya ja hankalin maniyatan da cewa su zama jakadu na gari idan suka je Kasa Mai Tsarki gudanar da aikin hajji.
- Buhari zai koma kasar waje sa’o’i kadan bayan dawowarsa
- Hajji 2022: Ranar Alhamis za a fara jigilar alhazan Najeriya
Ya kuma hori ma’aikatan hukumar da cewa kar su zama masu sa son rai ko cin zarafin alhzai a yayin gudanar da aikinsu, wanda zai zubarwa da hukumar kima da a idon mutane.
Batun hakan yana dauke ne a wata takardar bayan taro da babbar jami’ar hulda da jama’a ta hukumar Hauwa Muhammad, fitar da ta aikewa manema labarai a madadin babban sakataren hukumar.
A cewarsa, yanzu haka shirye-shirye sun yi nisa domin tuni an samarwa maniyatan masaukai masu kyau a Saudiyya, ana kuma yi maniyyata bita don sanin yadda za su gudanar da aikinsu a Saudiyya.
Sakataren ya sake jan hankalin maniyyata da su guji aikata ayyukan da suka saba doka da kuma guje wa safarar miyagun kwayoyi zuwa kasar ta Saudiya.
Daga nan sai ya gode wa gwamnan jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya, na zakulo hazikan mutane ya nada su a matsayin jagororin hukumar da suke taimaka masa wajen tafiyar da aikinsu yadda ya dace.