✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajj 2020: Alhazai sun fara isa Makkah

Alhazan aikin Hajjin bana sun fara sauka a Makkah daga filin jirgi na Sarki Abdulazeez da ke birnin Jidda na kasar Saudiyya. Ma’aikatar Aikin Hajji…

Alhazan aikin Hajjin bana sun fara sauka a Makkah daga filin jirgi na Sarki Abdulazeez da ke birnin Jidda na kasar Saudiyya.

Ma’aikatar Aikin Hajji da Umrah ta Saudiya ta ce alhazan na bana za su fito ne daga sassan kasar kadai, inda bayan saukarsu a Jiddah ake wucewa da su zuwa masaukansu a Makkah.

Bayan isarsu Makkah za su fara yin Umarah kafin shigowar ranakun aikin Hajji gadan-gadan.

Sanarwar da kasar ta fitar kan Hajjin bana ta hana duk wadanda ke wajen kasar halartar ibadar domin dakile yaduwar cutar coronavirus.

Kazalika ba a amince wa masu shekaru sama da 55 da masu fama da rashin lafiya zuwa aikin Hajjin ba.

Za kuma a yi wa dukkan maniyyata gwajin cutar kafin farawa, a lokacin da kuma bayan aikin Hajji.

Za kuma a tabbatar da matakan tsafta da kariya da kuma bayar da tazara a dukkan matakai da masaukai da tsarin sufuri na aikin Hajjin.

A ranar takwas ga watan Zhul Hajji alhazai za su bar masaukansu na Makkah zuwa Mina, inda daga nan za su wuce Arfa a ranar tara ga wata.

Za su zauna a Arfa daga safiya zuwa dab da Magaribar ranar tara ga watan.

Daga nan za su wuce su kwana a Muzdalifa sannan washegari su koma Mina su yi jifa da yanka da kuma aski.

A zamansu a Minan na biyu za su yi kwana biyu ko uku kafin su koma Makkah, inda daga karshen aikin Hajjin za su yi dawafin ban kwana.

A shekarar nan Saudiyya ta takaita aikin Hajji ga maniyyata kimanin mutum 10,000 domin kauce wa yaduwar cutar coronavirus.