✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajiya Salamatu Kana: Mata mu nemi na kanmu

Hajiya Salamatu Kana ta jima tana hada aikin gwamnati da kuma kasuwanci. A yanzu ita ce Babbar mai kula rumbun  kayayyakin ofishin Mataimakin Gwamnan Jihar…

Hajiya Salamatu KanaHajiya Salamatu Kana ta jima tana hada aikin gwamnati da kuma kasuwanci. A yanzu ita ce Babbar mai kula rumbun  kayayyakin ofishin Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa (Senior Store Keeper). Ta bukaci mata su  nemi na kansu, sannan ta bayyana yadda ilimi yake da mahimmaci ga rayuwar dan Adam

Tarihin rayuwarta
Sunana Hajiya Salamatu Kana. Na yi firamare a L.G.E.D Primary School Kana da ke karamar Hukumar Nasarawa. Daga nan na tafi Kwalejin Malamai ta Gwamnati da ke garin Nasarawa.  Na kuma yi difloma a makarantar Kimiyya da Fasaha a Lafiya, babban birnin Jihar Nasarawa. Na yi babbar difloma a makarantar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Filato da ke garin Jos.
A bangaren aiki kuma ina aiki da ma’aikatar kudi ta Jihar Nasarawa wanda a halin yanzu an turo ni nan ofishin mataimakin gwamna inda nake aiki a matsayin babbar mai kula da rumbun kayayyakin wannan ofishi (senior store keeper).
Burina lokacin da nake karama
A lokacin da nake sakandare na so in zama likita. Amma hakan bai yiwu ba, inda na tsinci kaina mai kula da rumbun kayayyakin ma’aikatar kudi.
 Abubuwan da na koya a wurin iyayena
A gaskiya iyayena sun koya mini abubuwa da yawa. Duk lokacin da na dawo daga makaranta sai su tura ni kasuwa, don na koyi kasuwanci. Amma a karshe dai ban ci gaba da harkokin kasuwancin ba sai aikin gwamnati.
 Lura da iyali
E,  to ‘ya’yana hudu,  maza uku; mace daya. Ina iya kokarina wajen tarbiyantar da su yadda ya kamata musamman a bangaren ilimi. Ni mace ce da ba ta wasa da harkokin ilimin ‘ya’yana. A koyaushe nakan tabbatar sun nemi ilimin zamani da na addini don ina da yakinin hakan ne babban gado da zan iya bar musu da zai taimaka wa rayuwarsu da na ‘ya’yansu nan gaba. Haka ina ba maigidana lokacin da ya kamata in ba shi, ina kuma girmama shi kamar yadda addinina watau Musulunci ya umurci mu mata mu yi wa mazajenmu a koyaushe.
 Babban kalubale da nake fuskanta a rayuwata
A gaskiya babban kalubale da nake fuskanta a rayuwata shi ne, bangaren neman ilimi. Allah ya yi ni mace mai matukar son neman ilimi, shi ya sa a kowane lokaci nakan yi kokari don in ci gaba da karatu na zamani da na addini don inganta rayuwata. Amma kamar yadda ka sani ba za ka hada wanda yake aiki, a lokaci guda yake karatu da wanda karatun kawai yake yi ba. Shi ya sa hakan ya zame min babban kalubale. Zan iya ba ka mitsali da ‘ya’yana, ga shi dai ni nake daukar nauyin karatunsu amma a halin yanzu suna so su wuce ni a bangaren neman ilimi. Saboda haka ina ganin wannan a matsayin babban kalubale gare ni.
 Yadda nake shawo kan kalubalen
Haka nema ya sa nakan kashe makudan kudade, da kuma lokacina wajen neman ilimi. A halin yanzu ina shirye-shiryen fara karatun digiri dina a babbar jami’ar Jihar Nasarawa da ke garin Keffi, inda zan rika tafiya a kowane karshen mako. Kafin wannan lokaci ma na riga na kammala karatuna a kan kwanfuyata a wata cibiyar koyar da ilimin kwafyuta da ke nan Lafiya. Na kuma kammala wani kwas a makarantar Kimiyya da Fasaha ta Lafiya.   Ina yin hakan ne don in shawo kan wannan kalubale.
kungiyoyi
Na shugabanci kungiyoyi da dama wadanda a halin yanzu ma ba zan iya tuna sunayen wasu daga cikinsu ba, sai dai idan na duba takarda. Daga cikin wadannan kungiyoyi akwai kungiyar C.T.L.S da kungiyar matan Afo ta Jihar Nasarawa. A takaice ire-irensu suna da yawa, amma dai na ba su gagarumar gudunmuwa wajen ci gabansu.
 Wuraren da nake sha’awa na je hutu
A duk lokacin da na samu hutu nakan tafi wani wurin hutu ne da ake kira “Wild Life Park” da ke garin Jos a Jihar Filato. Wuri ne da ake adana namun daji da na gida domin shakatawar masu yawon bude ido.
 Abin da nake so a tunani da shi
Kamar yadda na bayyana maka a baya. Iyayena sun koya mini harkokin kasuwanci, ko yanzu da nake aikin gwamnati ina hada wa da  kasuwanci don ina sha’awar harkar kasuwanci sosai. Kuma ‘yan kasuwa sukan kawo mini ziyara a gida ko a ofis, inda nake  ba su shawarwari game da harkokin kasuwanci. Saboda haka zan so a tuna da ni a matsayin mace da ta sadaukar da rayuwarta wajen daukaka harkokin kasuwanci a kasar nan.

Tallafi daga maigidana
A gaskiya ina samun tallafi sosai daga wurin maigidana. A kowane lokaci mukan hada kai wajen gudanar da harkokin gidanmu. Maigidana mutum ne da ya san ya kamata; wanda kuma ya san hakkin matarsa, shi ya sa a kullum nake girmama shi sosai saboda kyawawan halayensa. Abokin zama ne na kwarai, tun da muka yi aure ban taba samun matsala daga wurinsa ba. Na samu tallafi sosai daga wurinsa, ba ya kuma ba ni matsala.
 
Babbar kyauta daga maigidana
A gaskiya babu wanda ya taba ba ni kyautar da ba zan iya manta da ita a rayuwata ba kamar maigidana. Kodayake ya dade yana yi mini kyaututtuka daban-daban a lokuta mabambanta. Amma wannan babbar kyauta da nake maka bayyani ita ce, maigidana bai taba tafiya aikin hajji ba, amma kuma ya biya mini. Na je Saudiyya na sauke farali. Ka ga wannan kyauta ce da ba ni kawai ba kusan kowace mace Musulma ba za ta taba mantawa da ita a rayuwarta ba.
 Kayan koli
A cikin kayan koli na fi sha’awar hoda. Bayan na yi wanka na yi shiri sai in shafa hoda kafin in tafi wurin aikina. Amma idan ban shafa hoda ba ba na jin dadi.
 Halayen da na fi sha’awa a wurin mace
Halayen da na fi sha’awa ga mace su ne, in ga mace mai kwazo wajen neman na kanta. Matar da ba ta jira sai wata ya kare ta roki kudi a wurin mijinta. Ina so in yi amfani da wannan dama don in yi kira ga mata ‘yan uwana kada mu rika dogara da mazajenmu kawai. Amma mu mike tsaye mu nemi na kanmu. Gwamnotoci suna kokari wajen samar wa mata da sana’oin da za su inganta rayuwarsu. Amma abin bakin cikin shi ne yadda za ka tarar mace ta zauna ba ta yin komai sai dai ta rika kirga kwanan wata. Idan ya kare ta kai damuwarta wurin mijinta, shi ya sa a yau da zarar miji ba ya nan sai ka tarar an shiga wani mawuyacin halin.
 Tufafi
Na fi sha’awar tufafinmu na matan Arewa. Ban saba da tufafin Turawa ba don ni ba Baturiya ba ce.