✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajiya Kulu Musa Anka: Yadda siyasa ta kai ni gidan yari

Idan ba ka da galihu sai dai ka yi hakuri. Bayan sakamakon jarrabawarmu ya fito ne, aka manna sunana Kulu Musa na ci Birnin Kebbi,…

Idan ba ka da galihu sai dai ka yi hakuri. Bayan sakamakon jarrabawarmu ya fito ne, aka manna sunana Kulu Musa na ci Birnin Kebbi, amma washegari sai aka ce ba ni ba ce, Kulu Barau ce.

Hajiya Kulu Musa Anka tana daya daga cikin daraktoci mata na farko a Jihar Sakkwato, inda ta rike mukamin Darakta a Ma’aikatar Jin Dadin Ma’aikata a jihar, ta fara siyasa tun lokacin GNPP, inda tsoron gawa ya sanya ta daina aikin asibiti ta koma siyasa, ta yi bayanin yadda a dalilin siyasa aka kai ta gidan yari. Ga yadda hirar ta kasance:

Tarihina a takaice
Assalamu alaikum, sunana Kulu Musa Anka, mahaifina dan garin Anka ne a karamar Hukumar Anka da ke Jihar Zamfara, mahaifiyata ’yar garin Yabo ce da ke Jihar Sakkwato. Mahaifina ya hadu da mahaifiyata ne a lokacin da yake kasuwancin fata, sun yi soyayya har suka yi aure. Mahaifiyata ce matarsa ta biyu, yayan mahaifiyata ya yi Baturen fata fiye da shekara 20, tare da mahaifina suka rika fataucin fata a kan jakuna.
Bayan an haife ni sai ya koma gida; bayan wani lokaci ya rasu. Kodayake tun kafin ya rasu ya sanya ni makaranta, wato cikin mako na uku bayan na shiga makarantar firamare ne ya rasu, wasu Fulani suka kashe shi a gona bayan sun yi alkawarin za su kashe shi din, sanadiyyar haka aka dauki lokaci ana ta yake-yake, an fi shekara Fulani ba sa kawo nono garin Anka, a lokacin Sarkin Zamfara Amdu ne.
Rayuwar makaranta
Idan ba ka da galihu sai dai ka yi hakuri. Bayan sakamakon jarrabawarmu ya fito ne, aka manna sunana Kulu Musa na ci Birnin Kebbi, amma washegari sai aka ce ba ni ba ce, Kulu Barau ce. Na yi hakuri domin na san duk wurin da abincinka yake sai ka ci, ana cikin haka sai aka turo wa Sarkin Zamfaran Anka wata takarda cewa ana neman wasu mata za a bude WCWC, watau asibitin jin dadin mata da kananan yara, a wannan lokacin akwai wadanda suka tafi babu tsari, amma mu da za mu tafi sai iyayenmu suka ce mu tsare mutuncinmu, to da muka je sai muka rika jin tsoro,  a lokacin an bude makarantar kiwon lafiya, sai aka ba mu wata takarda daban muka sake shiga makarantar koyon aikin unguwar zoma, a nan na samu nasara sai muka fara, bayan mun kammala aka tura ni cibiyar kiwon lafiya da ke Gwadabawa, duk da haka hankalina bai kwanta ba, domin babu abin da ke ba ni tsoro tun ina karama kamar mutuwa, ina asibiti aka kawo wasu sun yi hadarin mota a kan wata gada da ake kira ‘gadar Zalzalu’ kuma ranar ni kadai ce, ganin yadda gawarwakin nan suke sai hankalina ya tashi, sai na ce kai bari in bar aikin, a lokacin marigayi Maccido shi ne kwamishinan lafiya, bayan na sanar da shi zan bar aiki ne, sai ya ce idan ina so zai mayar da ni Gummi, sai na ce gaskiya hankalina ya riga ya tashi, sai na dawo gida na yi aure, daga bisani sai na sake samun takardar karo karatu a Kaduna Poly, na karanta kwas din Duba-Gari da kuma ilimin manya. Na yi karatu har na kammala ba tare da wata matsala ba.

Ana cikin haka marigayiya Maryam Babangida ta fito da wani tsari da ke bukatar mata kuma duk Gummi ni kadai nake da wannan damar, daga nan aka tura ni Jami’ar Sakkwato, inda na ci gaba da karatu. Bayan wani lokaci marigayiya Maryam Babangida ta ce duk matsayin da namiji zai iya rike, to mace ma ya dace ta rike, sai aka kirkiro da ofishin jin dadin ma’aikata, inda aka ba ni darakta. Ina daga cikin mata daraktoci na farko a Jihar Sakkwato.
Gwagwarmayar siyasa
Na dade a harkar siyasa, ina siyasa gan ni tun lokacin Jam’iyyar GNPP, akwai kanin mahaifinmu mai suna M.Z Anka da ya yi takarar gwamna, tun fil’azal ba a raba siyasa da magudi, tun a wancan lokacin ana shiga gidajen sarakuna ana dangwala kuri’u, haka aka dangwala wa Jam’iyyar NPN a wancan lokaci. Ba na mantawa a lokacin ina Sakkwato ina neman karin girma, aka dauko takardata aka yi mini wasu tambayoyi, bayan na ba da amsa sai aka dauki takardata aka sanya karkashin kujera, aka ce in yi hakuri karin girma sai wata gwamnati ta zo, ban ce komai ba, bayan shekara shida na sake komawa, sai aka ce mini ai gwamnati mai zuwa da ake nufi, wato idan kanin mahaifinmu ya zama gwamna. Na dawo gida na fada wa maigidana, sai ya ce ai na fada miki ki yi hakuri, ana cikin haka mako biyu sai aka yi juyin mulki.
Haka aka yi ta tafiya da dadi babu dadi har lokacin da Mamuda Shinkafi ya zama gwamna, akwai lokacin da ya je Anka aka jefe shi, sai wasu suka ce a je a sanya wa shiyyar Magaji wuta, sai na yi na ce saboda me za a tafi a sanya wa uwayenmu tiyagas, abin dai ya tsaya gare shi, to wannan magana ta sake jawo mini matsala, ana cikin haka aka ce ga matasa sun taho za su kashe ni, na dauki mota na gudu wajen ’yan sanda, saboda abin da ya faru ga mahaifina na cewa wasu sun yi alkawarin shi ya sa na dauki wannan matakin.
Daga nan aka kai su kotu ana tuhumarsu da laifin sun yi furucin sai sun kashe ni, ana cikin haka sai aka kawo mini sammaci ana kara ta a kotu ta hudu, sun shigar da kara wai na same su a dabarsu na zage su, ina zuwa kotu duk da lauyan da aka dauka mini sai aka ce an ba ni mako biyu a gidan yari, sai na ce wa alkali saboda me ni ban kashe kowa ba, sai alkali ya ce kada in raina masa wayo, haka muka rika bugawa a karshe aka kai ni gidan yari, daurin mako biyu, a lokacin dana ba shi da lafiya, hakan ya kara daga mini hankali. Bayan na fito daga gidan yari, sai na daina tsoron kowa a harkar siyasa.
Mukaman da na rike
Na rike mukamin Kodineta a Hukumar UNICEF, daga baya na zama mamba a majalisar UNICEF. Na rike mukamin Shugabar Mata a Jam’iyya PDP a Jihar Zamfara.
Shawara ga mata
Ya kamata mata su yi wa kansu fada a harkar siyasa, domin suna shan wahala a siyasa, amma ba sa cin ribarta. Ya kamata su dubi abin da aka yi alkawarin za a ba su, zuwa yanzu nawa aka ba su, don haka ya kamata su fito a dama da su a harkar siyasa, ta haka ne za su kwato wa kansu ’yanci.
Ya kamata mata su nemi ilimi domin komai na rayuwa sai da ilimi ake yinsa, sannan ya kamata su rika yin kananan sana’o’i don dogara da kai, don kuma taimaka wa gida, kasancewar yanzu komai na rayuwa ya yi wahala, don haka akwai bukatar a rika taimaka wa maigida.