✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajiya Hajara: Ilimi ne ginshikin zaman duniya

Hajiya Hajara danyaro ita ce mai bai wa Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Almakura shawara a kan al’amuran tabbatar da adalci ga  jinsuna (Gender Ekuality).…

Hajiya Hajara danyaro ita ce mai bai wa Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Almakura shawara a kan al’amuran tabbatar da adalci ga  jinsuna (Gender Ekuality). A tattaunawarta da wakilinmu ta bayyana tarihin rayuwarta da wasu batutuwa. Ga yadda hirar ta kasance:

Tarihina
Da farko dai sunana Hajiya Hajara danyaro Ibrahim. An haife ni a nan Nasarawa Hedkwatar karamar Hukumar Nasarawa a Jihar Nasarawa. Na yi karatun firamari a kofar Kudu a nan Nasarawa. Daga nan na wuce sakandare a G.S.S. Nasarawa. Na ci gaba a makarantan kimiyya da fasaha ta Gwamnatin Tarayya ita ma a nan Nasarawa, inda na samu babban difloma.
Bayan haka ne, sai na yi aikin banki na wani lokaci a nan Nasarawa, inda na kai matsayin akanta. Daga nan sai na shiga harkar siyasa, inda na tsaya takarar kansila a karkashin jam’iyyar UNCP inda aka ba ni lakabin “Fatari mai ba wanda kashi”. Ban samu nasara a zaben ba, sakamakon magudi da aka yi mini a lokacin. Daga nan na samu mukamin shugabar matan jam’iyyar UNCP. Na kuma kasance mace ta farko da ta rike mukamin shugabar matan jam’iyyar PDP a jihar nan, inda bayan na kammala wa’adina aka sake zabena a mukamin karo na biyu a shekarar 2000. Na kuma kasance mace ta farko da tsohon gwamnan jihar nan, Sanata Abdullahi Adamu ya nada a matsayin kwamishinan Hukumar Zabe ta jihar nan a zamaninsa. Daga nan na shugabanci cibiyar yaki da jahilci a jihar nan. Na kuma shugabanci wata kungiya mai zaman kanta da ake kira “Project 50” wanda ke tabbatar an samu gwamna da bai wuce shekara 50 ba, a jihar nan. Da gwamnan jihar nan mai ci ya fito takara karon farko, ya nada ni a matsayin daraktan wayar da kawunan jama’a a kamfen dinsa. Da ya sake samun nasara a karo na biyu, sai ya nada ni mai bashi shawara ta musamman a kan harkokin jam’iyyun siyasa a jihar nan daga shekarar 2012 zuwa 2013.
Na kuma kasance Amira ta aikin hajji sau biyu a shekarar 2012 zuwa 2013. A yanzu dai ina rike da mukamin babban mai bai wa Gwamna Almakura shawara ta musamman a kan al’amuran tabbatar da adalci ga jinsuna.

Abin da ya sa na shiga siyasa
Na shiga siyasa ne don in taimakawa mata da yara musamman marasa galihu. A gaskiya a duk lokaci da na ga yadda wadannan mutane ke gudanar da rayuwansu zai inji tausayinsu, don mutane ne da ke matukar bukatar taimako. Na lura cewa siyasa hanya ce mafi sauki da zan iya taimaka wa galibinsu. Ban shiga harkar siyasa don in tara dukiya ko wani abu makamancin haka ba. Alhamdullilah, Allah Ya ba ni arziki daidai gwargwado. Sai dai kamar yadda na bayyana maka na shiga ne don in taimaka wa marasa karfi. Kuma ina so in yi amfani da wannan damar in yi kira na musamman ga gwamnatoti a dukkan matakai da masu hannu da shuni wadanda Allah Ya albarkacesu da arziki a kasar nan, cewa don Allah su rika tunawa da marasa galihu cikin al’umma. Kada su manta cewa arziki da Allah Ya ba su ba ya ba su da ’ya’yansu ne kadai ba. Amma don su taimakawa sauran jama’a ne musamman marasa karfi. Ta haka ne kawai za su samu albarkar Allah su kuma samu aljanna.

Sarautun gargajiya da nake rike da su
Su ne: Garkuwan Matan Nasarawa da Tauraruwan Matan Loko da Jarumar Matan Jihar Nasarawa da dai sauransu.  

Lambobin yabo da na samu
Jarumar Matan Afirka masu gina kasa da Ambasadan zaman lafiya ta kungiyar Unibersal Peace Federation a shekarar 2008 da Maman Afirka wanda kungiyar Election Communication Limited ke bayarwa da dai sauransu.

Wuraren da nake son ziyarta a lokacin hutuna
A gaskiya ba inda nake son tafiya a lokacin da na samu hutu kamar kasar Saudiyya. Nakan tafi kasar ne saboda na bautawa Allah da ya halicceni inda nake gode masa dangane da taimakona da yake yi a koyaushe. Duka wadannan nasarori da na cimma a rayuwana ba don ilimina, ko karfi ko kuma wayo na ba ne.

A’a, Allah ne ke ba ni wadannan nasarori saboda haka wajibi ne in ci gaba da bauta masa a koyaushe. Saboda haka a takaice dai kamar yadda na bayyana maka a baya nafi sha’awar ziyartar Saudiyya a lokacin hutuna don bautar Allah.

Shawarata ga ’yan uwana mata
Shawara ta garesu shi ne su tashi su nemi ilimin addini da na zamani don su ne ginshikin zaman duniya. Idan ba su da halin yin haka, sai su rungumi sana’a. Kada mace ta dogara ga mijinta kawai musamman a wannan zamani, don idan ta yi haka za ta fuskanci wulakanci. Hakazalika, wajibi ne ’yan uwana mata su tabbatar suna bai wa ’ya’yansu kyakkyawar kulawa ta wajen samar musu da ilimi mai inganci don ya taimakawa rayuwansu. Rayuwa ta canja yau sai da ilimi mutum ka iya yin komai saboda haka mata a rungumi ilimi don samun nasara a rayuwa.  
Abin da zan so a tuna ni da shi
Zan so a tuna ni a matsayin mace da ta yi duka mai yiwuwa wajen tallafawa mata musamman wadanda suka rasa mazajensu da nakasassu da kuma marasa galihu a cikin al’umma kamar yadda na bayyana a baya. Don na lura da dadewa cewa wadannan mutane suna matukar bukatar taimakon kowa cikin al’umma. Shi ya sa nake so yin amfani da wannan damar in yi kira na musamman ga masu hannu da shuni a kasar nan baki daya cewa don AlIah a rika taimakawa marasa galihu cikin al’umma a koyaushe. Kada mu manta cewa lalura ce ta same su ba yinsu ba ne. Kuma idan mun taimaka musu ba shakka za mu samu lada daga Ubangiji a nan duniya da kuma gobe kiyama.   

Iyali
Ina da aure, sunan mai gidana, Alhaji Abubakar Sadik Ubandoma. Kuma muna da ’ya’ya da shi.