Sabon Mashawarcin Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina kan harkokin tsaro da suka shafi yankin Daura, Alhaji Rabe Ibrahim Jibia ya riga mu gidan gaskiya.
Jibia ya yanke jiki ya fadi a babban masallacin Juma’a na Kumassie yayin halartar daurin auren ‘ya’yan mai ba wa gwamnan shawara kan harkoki a jihar, Alhaji Ibrahim Katsina.
- An kwaso ’yan Najeriya 255 da suka makale a Saudiyya
- Buhari ya taya Tinubu murnar zagayowar ranar haihuwa
- Guguwa ce ta sa na ‘samu juna biyu’ —Mace
- Ilimi Kanawa su ke bukata ba gadar sama ba —Kwankwaso
Da yake tabbatar da faruwa lamarin, Alhaji Ibrahim Katsina, ya ce, “tabbas a wurin daurin ‘ya’yana ne ya yanke jiki ya fadi yayin da yake gaisawa da mutane, inda aka dauke shi zuwa asibiti kuma a can ne likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.”
Alhaji Ibrahim Katsina, ya ce marigayi Rabe, na daga cikin sabbin hadimai da Gwamna Masari ya nada kan harkokin da suka shafi tsaro a jihar.
Ya mika sakon ta’aziyyarsa a madadin gwamnan jihar ga iyalan mamacin da kuma daukacin abokan aikinsa baki daya.