Hadimin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, kan harkokin siyasa, Sanata Babafemi Ojudu ya yi maraba da dawowar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zuwa jam’iyyar APC.
Ojudu, ya sanar da hakan ne a shafinsa na Facebook, inda ya bayyana Kwankwaso a matsayi jagora a siyasa, amma ya ce bai tabbatar da gaskiyar labarin na komawar tsohon Gwamnan APC ba.
- ’Yan damfara sun kirkiro shafin karya na ‘Daily Trust Hausa’
- Najeriya A Yau: Yadda Za A Bunkasa Fasahar Zamani Domin Samar Da Ayyukan Yi
Ya ce, “Labarin ya karade ko ina cewa jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Kwankwaso ya dawo jam’iyyarmu ta APC. Ban tabbatar da hakan ba har yanzu amma idan gaskiya ne ina masa lale maraba.
“Wannan zai kasance hukunci mai kyau a tafiyarsa ta siyasa. Jajirtaccen mutum, shugaba mai mabiya da yawan gaske zai taimaka mana wajen sake gina Najeriya,” kamar yadda ya wallafa.
Kazalika, Aminiya ta tuntubi Sunusi Bature Dawakin Tofa, Shugaban Sashe yada labarai daga tsagin Kwankwasiyya, ya bayyana labarin a matsayin na ‘kanzon-kurege’.
“Duk da cewar komai zai iya faruwa, amma har yanzu ba mu yanke hukuncin komawa wata jam’iyya ba.
“Labarin gaba daya ba gaskiya ba ne, Kwankwasiyya tafiya ce mai tsari, ba ma yanke hukunci haka nan, muna zama mu tattauna yadda makomarmu za ta kasance a siyasa.
“A wajenmu, wannan labari ya nuna yadda jagoranmu, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ke da tasiri a siyasar Najeriya, muna farin ciki yadda kowace jam’iyya ke son zawarcinsa,” inji shi.
Tun bayan ziyarar ta’aziyya da Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya kai wa Kwankwason bisa rasuwar kaninsa, aka shiga sharhi da tsokaci kan cewar Kwankwaso na iya komawa APC.