Mutum 997 sun rasu, wasu 4,317 sun jikkata sakamakon haddura a Jihar Kaduna, daga watan Janairu 2021 zuwa Oktoba 2022.
Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) reshen Jihar Kaduna, tace a cikin shekara biyun, an samu hadurra 1,163 a kwaryar Kaduna.
- Za a sayo wa makarantun FGC 18 motocin daukar marasa lafiya
- NAJERIYA A YAU: Yadda Tinubu Ke Shirin Bin Sawun Buhari
Mukaddashin Kwamandan hukumar a jihar, Garba Lawal, ya ce, “Kididdiga ta nuna haddurra da aka samu a hanyoyi a Jihar Kaduna a 2021 kadai sun kai 667, sannan 542 sun mutu, yayin da mutum 2,382 sun ji raunuka,”
“Ya zuwa Oktoba 2022, mutum 496 ne hadurra suka rutsa da su, mutum 455 sun mutu, sannan 1,935 sun jikkata.”
Jami’in ya ce, gudun wuce misali da oba-tekin ba bisa ka’ida ba da amfani da tayoyi marasa kyau, na daga cikin sabubbban haddura.
Ya bayyana haka ne a taron fadakarwa da hukumar ta shirya albarkacin Ranar Tunawa da wadanda hatsarin mota ya rutsa da su ta duniya ta 2022.
Ranar 20 ga Nuwamba ta kowace shekara aka ware don tunawa da ranar, wadda ta bana ta kasance a Lahadi mai zuwa.