✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hadarin mota ya yi ajalin mutum 4 a hanyar Ibadan

An gargadi direbobi kan daukar fasinjojin da suka zarce ka'ida.

Mutum hudu sun riga mu gidan gaskiya sakamakon wani hadarin mota da rutsa da su a kan babbar hanyar Ibadan da ke Jihar Oyo.

Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa FRSC ta ce lamarin ya auku a ranar Asabar.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, Kwamandan Rundunar FRSC reshen Asaba, DCC Bayode Olugbesan ya ce hadarin ya rutsa ne da wata motar bas kirar Toyota Hummer wadda ta taso daga Legas a kan hanyar zuwa Arewacin kasar.

Ya ce bincike ya nuna cewa hadarin ya auku ne a dalilin gudun wuce kima da dibar fasinjojin da suka zarce ka’ida.

A cewarsa, fasinjojin wadanda dukkansu maza ne sun hadarin ya rutsa da maza ne dake kan hanyar su ta zuwa Arewacin kasa.

Kwamanda Olugbesan ya ce “a lokacin da hadarin ya auku, motar tana dauke da mutane 20 da kaya a ciki ne a maimakon mutane 14 da doka ta amince a dauka a irin wannan mota.”

Ya ce tuni sun garzaya da sauran mutanen da suka samu raunuka zuwa asibiti domin ceto rayukansu a yayin da aka kai gawarwakin mamatan zuwa dakin ajiyar gawa na wani asibiti.

Ya ja kunnen direbobi da su guje wa tukin gudun wuce kima da motoci a kan hanya kuma su daina daukar fasinjoji da kayan da ya fi karfin motocinsu.