✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hadarin Mota ya yi ajalin mutum 10 a hanyar Kaduna

Hatsarin ya afku sakamakon daukar mutane fiye da kima.

Wani mummunan hadari da ya faru a daidai Tariyar Sarki kusa da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zariya, ya lakume rayukan mutum goma.

Aminiya ta gano cewa motar mai daukar mutum biyar, an makare ta ne da mutum 11 ciki har da direban motar.

Da ya ke tabbatar da afkuwar hadarin, Kwamandan Hukumar Hiyaye Hadura, reshen Zariya, Abubakar Tatah Murabus ya ce tuni su ka kai gawarwakin Asibitin Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Tatah Murabus, ya alakanta faruwar hatsarin da yadda aka makare ta da fasinjoji fiye da kima kari a kan gudun wuce sa’a da direban motar ke yi.

Ya ce sakamakon haka, direban ya daki ginin tsakiyar hanya inda motar ta yi tsalle sannan ta dira a can gefe, al’amarin da ya haddasa mutuwar mutum 10 nan take.

Ya sanar da cewa motar kirar Carina mai lamba KTL 251 QG, ta fito ne daga Kaduna a zuwa garin Bakori da ke Jihar Katsina, kafin afkuwar hatsarin.

Murabus ya yi bayanin cewa “Hadarin ya faru ne a ranar Asabar da misalin karfe 2 na rana a daidai Tariyar Sarki kusa da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zariya.

“Dukkan fasinjojin da ke cikin motar su 10 sun rasa ransu, sa’ilin da direban motar ne kawai mai suna Musa Ilyasu ya tsira da raunuka.

“Yanzu haka mun kai gawarwakin asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, har da direban da ya samu raunuka,” in ji shi.