✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hadarin mota ya lakume rayuka 5 a Kogi

Lamarin ya faru ne a lokacin da wasu motoci guda biyu da ke gudu suka yi taho-mu-gama.

Rahotanni sun bayyana cewa mutum 5 ne suka mutu a wani haɗarin da ya afku a tsakanin ƙauyukan Agbede da Agbadu, kan hanyar Lokoja zuwa Kabba a Jihar Kogi a ranar Alhamis.

Aminiya ta samu rahoton cewa lamarin ya faru ne a lokacin da wasu motoci guda biyu da ke gudu suka yi taho-mu-gama a lokacin da ɗaya daga cikin direbobin ya yi yunƙurin wuce wata babbar mota.

Kwamandan Hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Kogi, Samuel Oyedeji, ya ce motocin biyu da sun haɗa da wata ƙirar Ford Galaxy da wata Mazda.

Ya ƙara da cewa mutane 8 ne suka yi haɗarin, biyar sun mutu, uku kuma suka samu munanan raunuka.