✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hada-hadar kwayoyi: Hantar manyan ’yan sanda ta fara kadawa kan binciken Abba Kyari

Rahotanni daga Rundunar ’Yan Sanda ta kasa na nuna cewa hantar wasu manyan jami’anta ta fara kadawa a daidai lokacin da Hukumar Hana Sha da…

Rahotanni daga Rundunar ’Yan Sanda ta kasa na nuna cewa hantar wasu manyan jami’anta ta fara kadawa a daidai lokacin da Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta ke ci gaba da binciken dakataccen dan sanda, DCP Abba Kyari.

Hukumar dai na binciken Abba Kyarin da wasu mutum hudu da aka kama bisa zargin hada-hadar miyagun kwayoyi.

NDLEA dai a ranar Laraba ta sha alwashin cewa sai ta binciko lamarin tun daga tushe, inda tuni ta garzaya Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja domin ta samu izinin ajiye Kyarin sama da sa’o’i 48 a hannunta.

Bayanai dai na nuni da cewa wasu jami’an rundunar da suka taba mu’amala da Abba Kyari na can cikinsu ya duri ruwa, saboda fargabar kada ya ambaci sunansa a yayin tuhuma.

Wakilinmu, wanda ya ziyarci hedkwatar rusasshiyar rundunar yaki da ’yan fashi ta SARS, inda a can ne tsohon ofishin Abban yake, ya lura cewa batun binciken ne babban batun da ke labban jami’an.

Wakilin namu dai ya jiyo daya daga cikin jami’an na cewa, “Batun fa kullum kara kada mana hanta yake yi. Addu’ata har kullum ita ce kada wani ya je ya ambaci sunana.”

Shi kuwa wani jami’in cewa ya yi, “Dukkanmu masu tabbatar da doka ne, za mu sulhunta lamarin a karshe, amma NDLEA ta bi a hankali, kada su je su bata sunan oganninmu da sunan bincike. Babu fa wanda ba shi da kashi a gindinsa in dai a Najeriya ne.”

Aminiya ta gano cewa har yanzu ana ci gaba da hada-hada a rusasshiyar hedkwatar ta SARS, wacce a baya take yaki da matsafa da barayin motoci da garkuwa da mutane da fashi da makami da kuma tayar da bama-bamai.

Sai dai da wakilinmu ya tuntubi Kakakin ’yan sanda na kasa, Muyiwa Adejobi, don sanin inda rundunar ta kwana kan umarnin Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan Sanda ta Kasa (PSC) kan ta mika rahotonta a kan badakalar ta Abba Kyari cikin mako biyu, ya ce ba shi da masaniya a kai.

Amma ya yi alkawarin zai tuntubi wakilinmu daga bisani, ko da yake bai yi hakan ba, har zuwa lokacin hada wannan rahoton.