✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Habasha za ta rama cin da Najeriya ta yi mata a garin Kalaba -Kyaftin Debebe

Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Habasha mai suna Degu Debebe ya ce ko shakka babu za su yi duk mai yiwuwa su rama cin…

Kyaftin din Habasha Degu DebebeKyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Habasha mai suna Degu Debebe ya ce ko shakka babu za su yi duk mai yiwuwa su rama cin da kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta yi musu na ci 2-1 a wasan farko da ya gudana a Habasha a makon jiya.
Degu ya bayyana wa manema labarai jim kadan bayan an kammala wasa a tsakaninsa kasarsa da Najeriya cewa, kungiyarsa tana da karfin da za ta bi Super Eagles har gida ta yi mata lalata a wasa zagaye na biyu.
“Mun zubar da kwallaye a wasan farko amma za mu yi kokarin zura kwallaye a wasan na biyu da zai gudana a Najeriya”, inji kyaftin Debebe.
Sai dai dan kwallon ya ce za su koma teburin shawara don gano dabarun da za su bi wajen doke Najeriya a wasa zagaye na biyu da za a yi a ranar 16 ga watan Nuwamba mai zuwa a garin Kalaba.