Qasar Habasha ta koka kan yadda qalilan ne daga cikin baqin haure ’yan qasarta da ke aiki a Saudiyya suka dawo gida kafin qarewar wa’adin afuwar da Saudiyya ta yi musu a ranar Talatar da ta gabata.
A watan Maris ne Saudiyya ta ce waqanda ba su da cikakkun takardun zama a qasar ba za a kama su ba idan suka bar qasar cikin kwana 90, wa’wadin da ta qara da wata qaya, amma mutanen Habasha dubu 60 daga cikin dubu 400 kawai suka bar Saudiyya, inji gwamnatin Habasha.
Mutanen Habasha masu qimbin yawa ne suke zaune a Saudiyya suna aiki ba tare da izini ba, kuma duk wanda bai da izinin yana iya fuskantar zaman kurkuku ko kora daga qasar.
Ministan Sadarwa na qasar Habasha, Mista Negeri Lencho ya shaida wa BBC cewa yana jin tsorn abin da zai faru da mutanen qasarsa da har yanzu suke zaune a Saudiyya, inda ya ce wajibi ne su gaggauta dawowa “cikin gaggawa.”
“Za a kulle su a kurkuku kuma ba mu son ’yan qasarmu su shiga kurkukuk ko su haqu da cutarwa ta jiki ko tozartawa,” inji Mista Lencho.
qaya daga cikin waqanda suka dawo da ke aikatau a gidaje mai suna Nura Ahmed mai kimanin shekara 28 ta shaida wa wakilin BBC Emmanuel Igunza bayan ta sauka a Addis Ababa babban birnin qasar cewa: “Rayuwa tana da tsanani. Wani lokaci nakan zauna babu aikin yi saboda ba ni da cikakkun takardu, don haka ba ni da ikon yawatawa. Ba yadda mutum zai zauna lafiya a can.”
A shekarar 2013 mutanen Habasha da dama sun rasa rayukansu a wani faqa da ’yan sandan Saudiyya da suka kama su domin mayar da su qasarsu.
Mutane daga sassan duniya musamman Afirka da Asiya ta Kudu da Asiya ta Kudu maso Gabas suna regegeniya zuwa Saudiyya neman aiki, inda mahukuntan Saudiyya suka ce kimanin mutum miliyan qaya sne suke aiki a qasar ba tare da izinin zama a qasar ba.
Zuwa yanzu dai dubban mutane daga qasashen daban-daban sun yi amfani da wannan afuwa wurin komawa qasashensu ko kuma gyara takardun izinin zama a qasar.