Majalisar Dinkin Duniya ta ta ce yunwa da fari a kasar Habasa sun jefa miliyoyin ’yan kasar cikin mawuyacin hali.
Rhotanni daga Habasha sun nuna wannan shi ne fari mafi tsanani da kasar ta fuskanta cikin shekaru 40.
- ’Yan ta’adda sun yi garkuwa da matafiya a Katsina
- Buhari Ya Jinjina Wa Sarkin Musulmi Kan Wanzar Da Zaman Lafiya
Lamarin da ya sa Majalisar Dinkin Duniya yunkurawa don kai tallafin jinkai a kasar inda take sa ran mutum miliyan 17 su amfana, kamar yadda mai magana da yawun majalisar, Stephane Dujarric ya bayyana.
Dujarric ya shaida wa manema labarai ranar Laraba a New York cewa hakika, “Habasha na fuskantar wahalhalu wajen samun agaji,” daga mawuyacin halin da tsinci kanta.
Ya ce kawo yanzu mutum miliyan 24 ne suka samu tallafi a 2022 da suka hada da kayan abinci, kayan aikin noma, tsabtataccen ruwan sha da sauransu.
Ya kara da cewa, “Wasu sassan kasar na fuskantar hadarin ambaliya a ’yan makonni masu zuwa wanda ke iya shafar mutum sama da miliyan 1.7, ciki har da mata da kananan yara.”
A hannu guda, Sakataren Masalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya bayyana kaduwarsa kan yadda aka sake samun barkewarar tashin-tashina a wasu sassan kasar Habasha.
A kan haka ne ya yi kira da a dauki matakin gaggawa domin maido da zaman lafiya a yankunan da lamarin ya shafa.