Majalisar Dattawa ta tsawaita wa’adin karbar shawarwari kan gyare-gyare kundint tsarin mulki zuwa ranar 18 ga watan Satumba.
Kwamintin Gyaran Tsarin Mulki na Majalisar ya sanar da haka ne bayan matsin lamba da ya samu daga wurin ‘yan Najeriya da ke neman a kara lokacin.
“Ranar Laraba yakama mu rufe karbar takardu, amma muka samu umarnin cewa a ci gaba da karba zuwa ranar 18 18 ga Satumbal, 2020; ba mamaki matsin lambar da kwamitin ke fuskanta ne ya sa”, inji wani dan kwamitin da bai so a fadi sunansa ba.
A ranar Laraba Kwamitin ya sanar da dage rufe karbar takardun sakamakon matsi daga masu ruwa da tsaki ga shugaban Kwamitin, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar, Sanata Ovie Omo-Agege.
A ranar ce Omo-Agege ya bukaci masu neman a kirkiro sabbin jihohi da su tattauna da ‘yan majalisarsu da kuma sauran yankunan siyasar kasara.