✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwmanatin Kano ta rufe kamfanonin Ɗantata da Mangal

Gwmanatin Kano ta rufe kamfanin jiragen sama na Max Air mallakin surukin Kwankwaso da kamfanin Ɗantata kan taurin bashin kuɗaɗen haraji

Gwmanatin Kano ta rufe babban Ofishin Kamfanin Gine-gine na Ɗantata & Dawowa kan taurin bashin kudin haraji.

Kazalika Hukumar Tara Kuɗaɗen Shiga ta Jihar Kano (KIRS) ta rufe hedikwatar kamfanin jiragen sama na Max Air da kuma kamfanin shinkafa na Northern Rice a Oil Mill, kan rashin biyan haraji.

Daraktan Kula da Basuka na Hukumar, Ibrahim Abdullahi ya ce bayan samun umarnin kotu ne aka rufe kamfanonin.

Ya ce an rufe kamfanin Ɗantata & Sawoe mallakin hamshaƙin attajirin Kano, Alhaji Aminu Ɗantata ne kan bashin harajin albashi (PAYE) na shekara biyu (2021-2022) da ya kai Naira miliyan 241.

Kamfanin Max Air, mallakin Alhaji Sagiru Barau Manual babban attajirin Jihar Kastina — kuma surukin uban gidan gwamnan Kano mai ci Sanata Rabiu Musa Kwankwaso — kuma an rufe shi ne kan taurin bashin harajin shekara biyar (2017 zuwa 2022).

Jami’in ya ce an rufe kamfanonin ne bayan an yi ta rubuta musu takardu su biya kuɗaɗen ba tare da nasara ba.

Ya ce dukkansu za su ci gaba kasancewa a rufe har sai sun biya kuɗaɗen, yana mai cewa yin hakan ya zama dole domin tabbatar da ba sa ƙwarar jihar a kuɗaɗen harajinta domin samar da ayyukan cigaban al’ummar.