✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwarzon Gasar Marubuta ta Najeriya ya karbi kyautar dala 100,000 daga NLNG

Editan Shafin Adabi na jaridar Daily Trust kuma marubuci, Abubakar Adam Ibrahim ya karbi kyautar kudi dalar Amurka 100,000 (kimanin Naira miliyan 40), sakamakon lashe…

Editan Shafin Adabi na jaridar Daily Trust kuma marubuci, Abubakar Adam Ibrahim ya karbi kyautar kudi dalar Amurka 100,000 (kimanin Naira miliyan 40), sakamakon lashe gasar adabi ta bana da ya yi, wacce kamfanin NLNG (Kamfanin Samar Da Iskar Gas Na Najeriya) ke daukar nauyin gudanarwa duk shekara.
Gasar, wacce ake gudanarwa kowace shekara, ana zabar littafin labarin kirkira da ya zo na daya a cikin jerin littattafan da suka fafata, bayan alkalai sun duba rubucen-rubucen marubutansu.
A wannan shekarar, an yi bikin bayar da kyautar ne a ranar Talatar da ta gabata, a dakin taro na hukumar sojojin sama da ke Kado, Abuja, inda marubuci kuma dan jarida Abubakar Adam Ibrahim ya lashe gasar, ya zo na daya da littafinsa mai taken “Season of Crimson Blossoms.”
Da yake jawabi a wajen taron, Abubakar ya hori iyaye da su daina hana ’ya’yansu zabin aikin da suke so, inda yake cewa: “Ba wai magana a kaina ba ne, maganarmu ce baki daya. Wajen da mutum ya taso, addininsa ko yarensa ba za su hana shi zama abin da yake so ya zama ba a rayuwa. Don haka ya kamata iyaye su taimaka wa ’ya’yansu wajen cin ma burinsu.”
Haka nan, a karshen jawabinsa, ya gode wa iyayensa cikin tattausar murya, inda ya yaba wa mahaifiyarsa da take zaune a cikin dakin taron da matarsa da abokanen arziki da abokanen aiki. Ya kuma yaba wa kamfanin da ya wallafa littafin da kuma wadanda suka taimaka wajen ganin an buga littafin, inda a karshe ya ce: “Na gode, na gode, na gode!”
A nasa jawabin a wajen taron, Shugaban kamfanin Media Trust Malam Kabiru Yusuf, ya ce kamfanin zai ci gaba da tallafa wa ma’aikatansa da sauran ’yan Najeriya a fagen rubuce-rubuce da sauran bukatu irinsu, karfafa masu gwiwa.
“Wannan kamfanin na alfahari da Abubakar da ya yi wannan gagarumin aiki na rubuta wannan littafi da ya zama zakaran gwajin dafi. Muna fata mun samar da wata dama da za ta taimaka wa matasa kuma ta shirya su wajen cin ma burinsu na rayuwa, ba wai a bangaren aikin jarida ba kawai, har ma da bangaren rubuce-rubuce da kirkira-kirkire. Dan haka muna taya Abubakar murna da samun wannan kyauta kuma wannan ya kara tunatar da mu cewa aikinmu ba wai mu fitar da jarida ba ne kawai, har ma da hada mutane wadanda za su amfani mutane a bangarori daban-daban na rayuwa.” Inji shi.
Taron dai ya samu halartar mutane da yawa, wadanda suka hada da Ministan Watsa labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, Shugaban kamfanin Media Trust mai wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya, Malam Kabiru Yusuf, Babban Edita kuma Babban Jami’in Gudanarwa na kamfanin na Media Trust, Malam Mannir dan Ali, Farfesa Jerry Agada, Farfesa Isidore Idiala, Jakadan Ingila a Najeriya, mahaifiyar Abubakar, matarsa Maryam da ’ya’yansa Faris da Suhaila, abokanan aikinsa na kamfanin Media Trust, ’yan uwa da abokan arziki.