✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwarzon Aminiya na Shekarar 2022

A shekarar 2022 Aminiya ta kawo muku labaran mutane daban-daban wadanda suka taka rawar gani a fannoni daban-daban. Wasu daga cikin wadannan mutane sun taka…

A shekarar 2022 Aminiya ta kawo muku labaran mutane daban-daban wadanda suka taka rawar gani a fannoni daban-daban.

Wasu daga cikin wadannan mutane sun taka rawa ne wajen ayyukan ciyar da al’umma gaba, wadansu sun kafa tarihi, wadansu sun tari aradu da ka don ganin an yi abin da ya dace, wadansu kuma wata bajinta suka yi.

Kuma mun kawo muku labaran wadannan mutane a kafofinmu daban-daban, kama daga jarida zuwa ga shafinmu na intanet da kafofinmu na sada zumunta.

Don haka ne a shirye-shiryenta na kawo muku rahotanni na musamman a kan muhimman abubuwan da suka faru a 2022, Aminiya ta yanke shawarar zaben daya daga cikin wadannan mutane a matsayin Gwarzon Shekarar 2022.

Rawar Gani

An sha samun labarai na zargin jami’an tsaro – musamman ’yan sanda – da harbe mutane don kawai wadannan bayin Allah ba su bayar da na-goro ba, ko kuma sun bayar, amma bai kai yadda aka bukata ba.

Bugu da kari, an sha jin labarin jami’an tsaron da aka kora daga aiki, ko Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta gurfanar a gaban kotu, saboda sun yi sama-da-fadi da dukiyar al’umma ko sun keta doka don su samu abin duniya.

Na baya-bayan nan a cikin irin wadannan jami’ai da ake zargi shi ne DCP Abba Kyari – wani dan sanda da ’yan Najeriya da dama suke yi wa kyakkyawan zato saboda himma da kokarinsa – wanda aka zarga da hulda da wasu “bata-gari”.

A irin wannan yanayin ne sai ga labari cewa an samu wani dan sanda wanda aka bai wa hancin dala tana gugar dala, har Dalar Amurka 200,000 (kusan Naira miliyan 90), amma ya ki karba.

Wannan lamari ya bai wa ’yan Najeriya da dama mamaki, ya bai wa wasu sha’awa, ya kuma bai wa wasu kwarin gwiwa cewa har yanzu akwai na-gari a tsakanin jami’an kasar.

“Ina ma duk ’yan sandan Najeriya, da ma sauran jami’ai a kasar, haka suke”, abin da wadansu suke cewa ke nan.

A wannan zamamanin, kuma bisa la’akari da halin da ’yan sanda suke ciki ta fuskar yalwar albashi, samun wanda zai aikata abin da wannan dan sanda ya yi sai an tona.

Gwarzon Shekarar 2022

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yana mika lambar yabo ga ACP Daniel Itse Amah

Wadannan su ne dalilan da suka sa CSP (a da) ko ACP (a yanzu) Daniel Itse Amah, wanda Babban Jami’in Yankin Bompai na Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ne, ya zama Gwarzon Shekarar 2022 na Aminiya.

An kuma zabe shi ne daga cikin mutum bakwai wadanda suka hada da:

  1. Kabiru Musa Jammaje, marubuci kuma mai shirya finafinai: Yana kokarin inganta ilimin marasa galihu, musamman marayu, ta hanyar ba su tallafin karatu a makarantun da ya assasa da kuma wayar da kan talakawa kan muhimmancin ilimi, musamman a fina-finansa.
  2. Alhaji Dahiru Barau Mangal, dan ksuwa: An ambace shi ne saboda yadda yake taimakon talakawa ta hanyar sama musu ayyuka da sana’o’i; misali, ya raba wa matasa motoci su hada masa kudin a kan farashin sari a 2022, sannan yana raba wa talakawa abinci kullum a gidan mahaifiyarsa.
  3. CSP Daniel Itse Amah, Babban Jami’in Yankin Bompai na Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano: Duk da kaurin sunan da ’yan sanda suka yi wajen karbar na-goro, shi juya baya ya yi ga hancin Dala 200,000.
  4. Honorebul Femi Gbajabiamila, Shugaban Majalisar Wakilai ta Tarayya: Duk wani yunkuri da aka yi na shawo kan Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta janye yajin aikin da ta yi wata takwas tana yi ya ci tura. Amma da Mista Gbajabiamila ya sa baki, cikin dan kankanin lokaci aka kawo karshen lamarin.
  5. Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya), Shugaban Hukumar Yaki da Ta’ammali da Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA): A karkashin jagorancinsa, Hukumar NDLEA ta yi nasarar ganowa da kama masu fataucin miyagun kwayoyi da dama. Jami’anta ne kuma suka bankado badakalar da ake zargin CP Abba Kyari da hannu a cikinta.
  6. Alhaji Umar Makun Lapai, Sakataren Hukumar Alhazan Jihar Neja: Wani lokaci, tsoron kada su rasa kujerarsu, ko kuma tunanin wata alfarma da za su samu, kan hana ma’aikatan gwamnati taka wa na sama da su burki idan za su yi abin da bai dace ba. Mai yiwuwa Shugaban Hukumar Alhazai ta Kasa, Alhaji Zikrullah Hassan, ba shi da hurumin tsige Alhaji Umar. Amma dai Shugaban Hukumar Alhazan ta Jihar Neja ya yi rawar gani da ya hana Alhaji Zikirullah hayewa jirgin sama ya bar sauran alhazan Najeriya, talakawa, suna hamma a filin jirgi.
  7. Musa Sani, yaro mai basira: Musa Sani wani yaro ne dan shekara 13 wanda ya kwaikwayi ginin wata gadar sama a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno. A dalilin haka, Gwamna Babagana Umara Zulum ya dauki nauyin biya mishi kudin makaranta.

ACP Daniel Itse Amah

An haifi ACP Daniel Itse Amah ranar 7 ga watan Yulin 1981, a Karamar Hukumar Jos ta Gabas da ke Jihar Filato.

Ya fara aikin dan sanda a shekarar 2002 a matsayin sufeto a ranar 15 ga watan Agusta.

Ya yi aiki a wurare daban-daban, kafin daga bisani ya zama Babban Jami’in Yankin Bompai na Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano.

ACP Daniel ya shahara ne bayan bajintar da ya yi ta fatali da hancin makudan kudi, kuma ma Dalar Amurka.

Rahotanni sun ruwaito cewa an yi yunkurin ba shi hancin kimanin Dalar Amurka 200,000, wanda ya kai kusan Naira miliyan 90, amma ya ki karba don kare martabar aikinsa.

Wannan ya sa Hukumar da ke Kula da Al’amuran ‘Yan Sanda (PSC) ta ba shi lambar yabo tare da kara masa girma daga mukamin Babban Suferitanda, CSP, zuwa mukamin Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda, wato ACP.

Jami’in ya kuma samu kyautar Naira miliyan daya daga Hukumar.

Har wa yau, Kungiyar da ke Fafutukar Wayar da Kai da Tabbatar da Adalci da Aikata Gaskiya (CAJA), da hadin gwiwar Cibiyar Habaka Dabarun Yada Labarai ta Penlight, ta gudanar da wani taro mai taken ‘Kare Mutunci a Matsayin Hanyar Yaki da Cin Hanci da Rashawa’, inda aka bayar da lambar yabo ga ACP Daniel Itse Amah a ranar 14 ga Disamba, 2022.

Aminiya ta ruwaito cewa a ranar 4 ga watan Oktoba ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bai wa ACP Amah lambar yabo ta Aiki da Gaskiya yayin wani taron kasa karo na hudu a kan yaki da cin hanci wanda Hukumar Yaki da Cin Hanci ta ICPC ta shirya.

Zaben Gwarzon Shekarar 2022

A matakin farko na zaben Gwarzon Shekarar 2022 na Aminiya, wakilanmu a fadin kasar nan da kuma ma’aikatanmu da suke Abuja ne suka bayar da sunayen mutanen da suke ganin sun cancanci wannan matsayi.

Wadannan wakilai da ma’aikata ne suka tattaro kuma suka rubuta labaran da muka bayar a kan wadannan bayin Allah.

Daga nan ne editocin Aminiya suka zauna suka yi nazari a kan dalilan da aka bayar na zaben ko wane daya daga cikin mutanen, sannan suka fitar da mutum uku.

Wadannan ukun – ACP Daniel Itse Amah da Honorebul Femi Gbajabiamila da Alhaji Umar Makun Lapai – an gabatar da su ga masu bibiyar kafofin sada zumunta na Aminiya don su zabi daya.

Honarebul Gbajabiamila ne ya zo na uku, bayan da kashi 4.3 cikin 100 na masu bibiyar shafukan namu da suka kada kuri’a suka zabe shi.

Sai kuma Alhaji Umar Makun Lapai, Sakataren Hukumar Alhazai na Jihar Neja, wanda ya zo na biyu da kashi 39.1 cikin 100.

Kashi 56.5 cikin 100 na wadanda suka yi zaben ne suka ce CSP ko kuma ACP Amah ne gwarzonsu, don haka ya zama Gwarzon Shekarar 2022 na Aminiya.

https://twitter.com/aminiyatrust/status/1608836009403486210?s=20&t=nPMD8UERB1elMpD6t7K9mw

 

Sakamakon kuri’ar da masu bibiyar shafukan Aminiya suka kada.

Sani Ibrahim Paki da Salim Umar Ibrahim da Elizabeth Fidelis sun taimaka wajen rubuta wannan rahoton.