✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwankin da ya shekara 2 da taya a wuyansa ya shaki iskar ’yanci

Jami’an kula da gandun daji a Jihar Colorado ta Amurka sun ce wani Gwanki da ya shafe shekara biyu yana gararanba da tayar da ta…

Jami’an kula da gandun daji a Jihar Colorado ta Amurka sun ce wani Gwanki da ya shafe shekara biyu yana gararanba da tayar da ta makale masa a wuya a yanzu dai ya shaki iskar ’yanci.

An dai hangi Gwankin, mai kimanin shekara hudu da rabi a Kudu maso Yammacin yankin Denver ranar Asabar, inda jami’an kula da gandun daji suka sami nasarar cire masa tayar.

Wannan ne dai karo na hudu da jami’an ke yunkurin cire masa tayar, amma ba su yi nasara ba.

Jaridar The Guardian ta Burtaniya ta rawaito cewa tilas sai da jami’an suka yanke masa kahunhuna biyar kafin su iya cire masa tayar saboda wayar cikinta ta ki yankuwa.

“Mun so a ce tayar muka yanke saboda mu kyale masa kahunhunansa, amma lamarin ya ci tura, dole sai da muka yanke su,” inji Scott Murdoch, wani ma’aikacin gandun daji.

Shi kuwa Dawson Swanson, wani abokin aikin Scott din cewa ya yi, “Na ji dadin kasancewar mai yin aiki a al’ummar da ta san mutuncin dabbobi. Mun sami damar cire masa tayar jim kadan da samun rahoton ganin Gwamnkin daga mazauna yankin.

“Mun samu kama shi lokacin da yake cikin wani garken ‘yan uwansa, wadanda yawansu ya kai kusan 40.”

Swanson da Murdoch sun cika da mamaki lokacin da suka ga Gwankin a yanayi mai kyau bayan shafe shekara biyu yana fama da tayar a wuya.

Ma’aikatan gandun dajin dai sun fara ganin Gwankin ne a watan Yulin 2019, lokacin da suke gudanar da wata kidayar manyan dabbobi a tsaunin Rocky, da ta awakai a tsaunin Evans.

Tun lokacin dai Gwankin yake ta gararanba a tsakanin kauyukan Park da Jefferson da ke Jihar ta Colorado.

Ma’aikatan dai sun ce suna ganin dabbobi da dama dauke tarkace kamar su karafa, katako, kwanduna, da dai sauran kayayyaki a jikinsu,.