✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnonin PDP za su yi zama kan matsalar tsaro da tattalin arziki

Jam'iyyar PDP na ganin gara jiya da yau a bangaren tsaro da tattalin arzikin Najeriya.

Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar PDP za ta yi taro a ranar Litinin kan sha’anin tsaro da tattalin arzikin Najeriya.

Daraktan-Janar na kungiyar gwamnonin, C.I.D. Maduabum ya ce za a yi taron a garin Ibadan na Jihar Oyo.

“Taron zai mai da hankali ne kan sha’anin tsaro da kuma irin koma baya da tattalin arzikin Najeriya  ke samu.

“Za kuma mu kara fadada hanyoyin taimakon gwamnatocin PDP don tabbatar wa ’yan Najeriya cewa babu wata mafita gare su face jam’iyyar,” a cewar Maduabum.

Ya ce ana sa ran gwamnoni 15 na jam’iyyar PDP za su halarci taron wanda Shugaban Kungiyar kuma Gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, zai jagorannta.

Shi kuwa, Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, zai kasance a matsayin mai masaukin baki.

Jam’iyyar PDP, kasancewarta babbar jam’iyyar adawa ga APC, ta dade tana sukar kamun ludayi mulkin Shugaba Buhari, musamman ta fuskar tsaro da tattalin arziki, wadanda PDP ke ganin gara jiya da yau.