Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar PDP za ta yi taro a ranar Litinin kan sha’anin tsaro da tattalin arzikin Najeriya.
Daraktan-Janar na kungiyar gwamnonin, C.I.D. Maduabum ya ce za a yi taron a garin Ibadan na Jihar Oyo.
- Nada Sarki Sanusi Khalifan Tijjaniyya alheri ne —Shehunnai
- ’Yan bindiga sun kashe manoma a Binuwe
- El-Rufai da Kungiyar Kwadago sun sa zare a Kaduna
- Cutar COVID-19 za ta tsananta a 2021 —WHO
“Taron zai mai da hankali ne kan sha’anin tsaro da kuma irin koma baya da tattalin arzikin Najeriya ke samu.
“Za kuma mu kara fadada hanyoyin taimakon gwamnatocin PDP don tabbatar wa ’yan Najeriya cewa babu wata mafita gare su face jam’iyyar,” a cewar Maduabum.
Ya ce ana sa ran gwamnoni 15 na jam’iyyar PDP za su halarci taron wanda Shugaban Kungiyar kuma Gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, zai jagorannta.
Shi kuwa, Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, zai kasance a matsayin mai masaukin baki.
Jam’iyyar PDP, kasancewarta babbar jam’iyyar adawa ga APC, ta dade tana sukar kamun ludayi mulkin Shugaba Buhari, musamman ta fuskar tsaro da tattalin arziki, wadanda PDP ke ganin gara jiya da yau.