✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnonin PDP za su yi taro ranar Laraba

Gwamnonin za su tattauna matsalolin jam'iyyar kafin taron Majalisar Zartarwa.

Gwamnonin da aka zaba karkashin jam’iyyar PDP  za su gana a ranar Laraba gabanin taron Kwamitin Zartarwa na jam’iyyar da aka tsara ranar 9 ga watan Satumba.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP, Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sakkwato, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Darakta-Janar na kungiyar, C.I.D Maduabum, ya fitar da sanyin safiyar Laraba a Abuja.

Sanarwar ta bayyana cewa Tambuwal ya tuntubi gwamnonin, inda suka kira wani taro na musamman da zai gudana a ranar Laraba da karfe 3 na yamma.

Taron, a cewar sanarwar, zai tattauna batutuwan da suka taso a jam’iyyar da kuma dabarun sake canza fasalinta kafin taron Kwamitin Zartarwa da za a yi ranar Alhamis.

Ya sake tabbatar wa dukkan mambobi da masu ruwa da tsaki da kuma gwamnonin jam’iyyar  aniyar shugabancin jam’iyyar na kasa wajen karbar madafun iko daga jam’iyyar APC.