✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnonin PDP na taro a Taraba

Gwamnonin waɗanda suka sauka a Filin Jirgi na Danbaba Suntai sun isa Jalingo a jirage aƙalla shida.

Gwamnonin jam’iyyar adawa ta PDP na taro a birnin Jalingo na Jihar Taraba.

Gwamnoni 9 daga cikin 13 na jam’iyyar na halartar taron wanda Gwamna Agbu Kefa na Taraba ke saukar baƙi.

Gwamnonin da ke halartar taron sun haɗa da Bala Mohammed na Bauchi da Ahmadu Umaru Finitir na Adamawa da Siminalayi Fubara na Ribas.

Sauran gwamnonin sun haɗa da Sheriff Oborevwori na Delta da Godwin Obaseki na Edo da Peter Mbah na Enugu da Dauda Lawal Dare na Zamfara da kuma Caleb Mutfwang na Filato.

Aminiya ta ruwaito cewa gwamnonin sun soma taron na sirri da misalin ƙarfe 2:00 na rana.

Bayanai sun ce gwamnonin waɗanda suka sauka a Filin Jirgi na Danbaba Suntai sun isa Jalingo a jirage aƙalla shida.

Ana sa ran wasu daga cikin gwamnonin za su halarci ɗaurin diyar gwamnan Taraba da za a gudanar a gobe Asabar.