✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Gwamnonin PDP na kawo cikas wajen magance rikicin makiyaya’

Tun bayan samun ’yancin kai babu abin da Gwamnonin PDP suka tsinana a Najeriya.

Fadar Shugaban Najeriya ta zargi gwamnonin jam’iyyar adawa ta PDP da kawo zagon kasa a kokarin da take yi na kawo karshen rikicin makiyaya a kasar.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Laraba, ya ce gwamnonin da aka zaba karkashin jam’iyyar PDP ba sa goyon bayan shirin kawo karshen rikicin makiyaya domin ceton rayuka da dukiyoyin al’umma.

Sanarwar na zuwa ne a matsayin martani bayan taron da kungiyar Gwamnonin PDP ta gudanar ranar Litinin a Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom.

“Gwamnatinmu ta samar da wata manufa ta kawo karshen kalubalen da makiyaya ke fuskanta amma gwamnonin PDP sun yi watsi da ita.

“Mun kawo dabarun da za a samar da matsuguni ga makiyaya don kawo mafita ga kalubalen da al’ummomi daban-daban da kasarmu ke fuskanta amma Gwamnonin PDP sun ki amincewa da su.

“Sun hana ’yan Najeriya ’yancinsu wanda kundin tsarin mulki ya yi tanadi, sannan babu abin da suka sa gaba face kira zuwa ga rarrabuwar kawuna tsakanin kabilun kasar.

“Tun bayan samun ’yancin kai da Najeriya ta yi, babu wani ci gaba da suka kawo ko samar da mafita ta wata matsala da kasar take fuskanta,” inji Shehu.

Hadimin shugaban kasar ya ce babu wata mafita da Gwamnonin jam’iyyar adawar suka kawo yayin da da kasar take fama da kalubalen annobar Coronavirus.