Bayan da suka kamala taron su a Uyo fadar gwamnatin jihar Akwa Ibom gwamnonin shiyyar Kudu maso Gabas dana kudu maso kudu daukacin su sun bukaci gwamnatin tarayya ta kara musu kaso cikin abin hasafi na kasa da ta ke bai wa gwamnonin jihohin a cewarsu, bai ishe su ba.Gwamnonin sun bayyana bukatar su ce karara a jawabin bayan taro da suka raba wa manema labarai a uyo bayan kammala taron da suka yi.
Takardar jawabin bayann taron da mai masaukin bakin kuma Gwamnan Jihar Akwa Ibom Udom Emmanuel, ta yi nuni da cewa: “Duk da tashin farashin da manfetur ya yi a kasuwannin duniya kudi da gwamnatin tarayya take ba su daga cikin asusun tarayya abin da ake ba mu ba ma ganinsa a kar, don haka muke kira ga Gwamnatin Muhammadu Buhari da ta yi mana kari”inji su.
Haka nan kuma sun jawo hankalin gwamnatin tarayya da ta gyara filayen jiragen saman Enugu Imo da ke yankunan su da kuma hanyoyin motar da ke yankin suka lilace.
Har ilayau sun koka da irin rikon sakainar kashin da gwamnatin tarayya ke yi wa yankunansu.Gwamnonin Jihar Imo Rochas Okorocha da Nyesom Wike na Jihar Ribas da kuma Seriake Dickson,na Bayelsa kana kuma da Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu.
Sauran sune Ifeanyi Okowa na Jihar Delta, Okezie Ikpeazu na Jihar Abiya da Ibara Esu mataimakin Gwamnan Jihar Kuros Riba da Doktar Nkem Okeke, Mmataimakin Gwamnan Anambra.