Gwamnonin jihohin arewacin Najeriya sun amince za su sayo motocin tafi da gidanka na gwajin cutar coronavirus wadanda za su yi amfani da su wajen yi wa jama’a gwajin cutar a yankunan karkarar jihohin.
Gwamnonin sun dauki wannan matsaya ne yayin taron da suka gudanar ta hanyar waya ranar Juma’a a kokarinsu na dakile yaduwar annobar.
Taron gwamnonin ya kuma bayyana matukar farin cikinsa da matakin gaggawa da Shugaba Muhammadu Buhari ya dauka a kan abin da yake faruwa na yaduwar wannan cuta a jihar Kano.
Gwamnonin sun koka da yadda har yanzu mutane suke karya dokar rufe iyakokin jihohi, ta hanyar amfani da manyan motoci wajen shiga jihohin, lamarin da ke dada kawo yaduwar wannan cuta.
Sun amince su kara jami’an tsaro na sa-kai da ’yan sintiri da sarakunan gargajiya a kan iyakokin, don ganin ana aiki da dokar rufe kofofin shiga da fita.
Haka kuma sun yanke shawarar rufe iyakokin jihohin yankin, tun daga karfe 6 na yamma zuwa karfe 7 na safe, don magance wannan matsala.
An gudanar da taron ne dai a karkashin jagorancin shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan jihar Filato Simon Bako Lalong.