Gwamnonin Arewacin Najeriya sun ɗaura ɗamarar haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya da sauran masu ruwa da tsaki domin yaƙi da matsalar rashin abinci mai gina jiki a yankin.
Gwamnonin sun ƙuduri wannan aniyar ce yayin wani taron tattaunawa kan ƙarancin abinci mai gina jiki mai taken “Karuwar Rashin Abinci Mai Gina Jiki a Arewa: Magance Matsalar Da Ta Tunkaro.”
Cibiyar tsare-tsare da gudanar da mulki ta Athena tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Lafiya da Walwalar Jama’a ta Tarayya ne suka shirya taron wanda ya gudana a Otel ɗin Transcorp da ke Abuja, babban birnin kasar.
- ’Yan bindiga sun sace hakimi da manoma 2 a Kaduna
- Ruwan sama ya yi ajalin mutum 3, ya lalata gidaje 50 a Yobe
Tun a farkon watan Yuni ne ƙungiyar likitoci ta Médecins Sans Frontières, wanda aka fi sani da Doctors Without Border da ke gudanar da ayyukan jin-ƙai ta fannin kiwon lafiya ta ce cibiyoyin karɓar magani a Arewacin Nijeriya sun samu ƙaruwar yara masu fama da ciwon rashin abincin mai gina jiki.
Ƙungiyar ta ce, a yanzu adadin yaran da ke fama da wannan matsalar da ke jefa rayuwa cikin haɗari ta haura da fiye da kashi ɗari idan an kwatanta da shekarar da ta gabata.
MSF ta ce wannan wata alama ce mai ban tsoro da ke da alaƙa da talaucin da ake fama da shi a Arewacin ƙasar tun kafin zuwan lokacin kaka, da kuma ƙaruwar matsanancin rashin wadatar abinci da ake fuskanta, wanda a kan saba gani a watan Yuli.
“A yanzu muna jinyar marasa lafiya a kan katifu da aka shimfiɗa a ƙasa saboda cibiyoyinmu sun cika. Yara da yawa suna mutuwa.
“Idan ba a dauki mataki gaggawa ba, rayuka da yawa suna cikin haɗari.
“Ya kamata duk mu tashi tsaye domin ceto rayuka da ba wa yaran Arewacin Nijeriya damar girma cikin wadatar abinci, ba tare da fuskatar ƙalubale ko mutuwa ba,” in ji Wakilin MSF a Najeriya, Dokta Simba Tirima.
A jawabinsa na buɗe taro, shugaban Cibiyar Athena, Osita Chidoka, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su haɗa kai domin ceto rayukan yaran Nijeriya da ke fuskantar matsananciyar yunwa da rashin abinci mai gina jiki.
Chidoka wanda shi ne ya assasa cibitar ta Athena ya kuma jaddada buƙatar a gaggauta haɗa kai domin magance wannan matsala mai tsanani.
Ya bayyana ƙaruwar rashin wadatar abinci a yankin na Arewa a matsayin abin tsoro da ke buƙatar ɗaukar mataki na gaggawa.
Chidoka ya ambato buƙatar wayar da kan kasa dangane da matsalar rashin wadatar abinci, yana mai jaddada muhimmancin haɗa kai tsakanin gwamnatocin tarayya da na jihohi, da kuma abokan ci gaba na ƙasa da ƙasa.
“Wannan taron ya shafi kowa domin burinmu shi ne wayar da kan ƙasa dangane da wannan matsalar da kuma neman hanyoyin magance matsalar domin tabbatar da cewa mutanen mu ba za su sha wahala a dalilin yunwa mai tsanani ba,” a cewar Chidoka.
A nasa ɓangaren, Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Farfesa Ali Pate, ya bayyana wasu tsare-tsare na gwamnati, ciki har da kafa wuraren jinya da aka tanada da abinci mai gina jiki da aka shirya a cikin gida domin jinyar masu fama da cutar matsananciyar yunwa a yankin Arewa maso Gabas.
Ministan ya bayyana giɓin da ke akwai a Arewa maso Yamma da sannan ya taɓo batun yadda za a samu tallafi don cike waɗannan giɓin, ciki har da samar da miliyoyin magungunan ƙarin sinadaran abinci domin rabawa a jihohin yankin.
Ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da dala biliyan 11 da za a raba wa jihohin domin tunkarar wannan matsala.
“Yaranmu na daya daga cikin muhimman dukiyoyin da wannan kasa ke da shi.
“Wannan kwamiti mai ɓangarori da dama yana haɗa ma’aikatu kamar su noma, lafiya, da ilimi domin yaƙar matsalolin da ke haifar da rashin wadatar abinci.
“Wannan shiri da muka ɗauko yana cikin sahun wani yunƙuri na tabbatar da wadatar abinci da inganta lafiyar ‘yan Najeriya na tsawon lokaci.
“Wani kaso mai yawa na kuɗaɗen da aka amince za a tura shi ne domin inganta cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko 1,200 a faɗin kasar.
“Waɗannan cibiyoyi za su fi samun kayan aiki don samar da muhimman ayyuka, ciki har da jinyar masu fama da matsananciyar yunwa.
“Haka kuma, Asusun Tallafa wa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF ya yi gwamnati alƙawarin dala miliyan 60 wanda za a yi amfani da shi wajen sayen abinci mai gina jiki da sauran kayan da ake buƙata”, in ji Pate.
Shi ma da yake jawabi a wajen taron, Ministan Noma, Abubakar Kyari, wanda Daraktar Gina Jiki da Tsaron Abinci ta Ma’aikatar, Hajiya Fatima Sugra ta wakilta, ya bayyana shirin samar da abinci na dogon zango, karfafawa da kuma jaddada amfani da hanyoyin noma masu ɗorewa.
Ya ce, “Matakan gaggawa sun haɗa da raba irin shuka ingantattu da takin zamani ga manoma, inganta gonakin gida, da bunƙasa kiwon dabbobi.”
Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Bago, ya jaddada muhimmancin bunƙasa harkokin noma a matsayin wata dabara ta yaƙi da rashin wadatar abinci da yunwa a yankin.
Bago ya jaddada buƙatar inganta hanyoyin noma domin tabbatar da samar da abinci mai gina jiki mai inganci.
Ya lura cewa magance matsananciyar yunwa tana da nasaba da magance matsalar wadatar abinci, wanda ya dogara sosai kan ɓangaren noma.
“Gwamnatinmu ta mayar da hankali kan faɗaɗa tattalin arzikin Jihar Neja ta hanyar inganta samar da amfanin gona, musamman wajen sanya injinan harkokin noma da zai ba da gudunmawar biyan buƙatunnmu na ciki gida har ma da na waje.
“Abun mamaki shi ne Jihar Neja na da injinan noma da taraktoci fiye da sauran jihohin Nijeriya baki daya, wanda hakan ke nuna ci gaban da yankin ya samu a fannin bunkasa harkokin noma,” in ji shi.
A nasa ɓangaren, Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya yi kira da a mayar da hankali kan yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, yana mai kira ga abokan ci gaba da sy guji fifita yankin Arewa maso Gabas kaɗai.
Gwamnan Jihar Katsina, Umar Dikko Radda, ya jaddada buƙatar ɗaukar mataki nan da nan, yana mai alƙawarin bayar da tallafin kudi domin shirin a jiharsa.
Shi ma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, wanda mataimakinsa, Umar Abubakar Tafida, ya wakilta, ya sake jaddada shirin gwamnatin jihar na haɗa kai da masu ruwa da tsaki don taimakon ‘yan kasa masu fama da rashin wadatar abinci.
A halin yanzu, MSF ta lura cewa kimanin yara miliyan 2.6 a Nijeriya na fama da matsanancin ƙarancin abinci mai gina jiki, da kuma ƙarin wasu miliyan tara da ke fama da matsakaicin ƙarancin abinci mai gina jiki.
Wakiliyar Bankin Duniya mai kula da shirin yaƙi da rashin abinci mai gina jiki a Nijeriya, Ritgak Tilley-Gyado, ta ba da shawarar inganta ayyukan shugabanci da haɗin kai, samar da shirye-shiryen kariya na zamantakewa da kuma amfani da sabbin hanyoyin da ake buƙata domin samar da abinci mai gina jiki domin inganta lafiyar al’umma.