✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnonin Arewa na taron gaggawa

Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya sun fara taron gaggawa a yayin da yanayin zanga-zangar EndSARS ke sanya damuwa a sassan kasar. 15 daga cikin Gwamnonin na…

Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya sun fara taron gaggawa a yayin da yanayin zanga-zangar EndSARS ke sanya damuwa a sassan kasar.

15 daga cikin Gwamnonin na halartar taron da ke gudana a Gidan Gwamnatin Jihar Kaduna na Sir Kashim a ranar Laraba.

Fara taron ke da wuya sai gwamnonin suka bukaci a ‘yan jarida su ba su wuri domin su tattauna.

Mahalarta zaman sun hada da Shugaban Kungiyar, Simon Lalong na Jihar Filat, Gwamna Aminu Tambuwal na Sakkwato, Mai Mala Buni na Jihar Yobe, Muhammad Inuwa Yahaya na Gombe, da Abdulrahman Abdulrazaq na Jihar Kwara.

Sauran su ne Gwamna Atiku Bagudu na Kebbi, Abdullahi Sule na Nasarawa, da Babagana Zulum na Borno.

Akwai kuma Mohammed Bello Matawalle na Jihar Zamfara sai kuma mataimakan gwamnonin Kogi, Kano Katsina da Kaduna.