Gwamnonin Arewacin Najeriya na taro a Kaduna don tattauna batutuwan da suka dabaibaye batun karbar harajin kayayyaki na VAT.
A ranar tara ga watan Agusta ne dai Babbar Kotun Jihar Ribas ta bayar da wani umarni da ya hana Hukumar Tattara Haraji ta Kasa (FIRS) daga karbar harajin na VAT a Jihar ta Ribas, tare da umartar Jihar da ta ci gaba da karba da kanta.
- Mahara sun kashe mutum 30 a Kudancin Kaduna
- Mun sami rahoton aikata fyade sau 652 a shekara biyu – Cibiya
Biyo bayan haka ne ita ma Jihar Legas ta bi sahu, ko da yake daga bisani wata kotun daukaka kara ta umarci Jihohin da su dakata bayan da Gwamnatin Tarayya ta daukaka kara a kan hukuncin.
Da yake jawabi yayin taron na gaggawa da ke gudana a Gidan Gwamnatin Jihar Kaduna, Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, kuma Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong ya ce taron zai kuma tattauna wasu batutuwan da suka shafi matsalar tsaro da ci gaban yankin.
Gwamnan, wanda ke jawabi gabanin fara taron da ke gudana a cikin sirri, ya ce shugabannin za su tattauna sauran batutuwan da suka shafi kasa da suka bijiro a kwanan nan don su fitar da matsayarsu a kai.
Kazalika, ya ce yankin zai kuma ce yankin zai fito da hanyoyyin da za su tabbatar an kare muradunsa a matakin kasa.
Gwamna Lalong ya kara da cewa taron zai tattauna kan ci gaban da aka samu ya zuwa yanzu a kan wasu batutuwa da aka kafa kwamitoci a taronsu na watan Fabrairu.
Manyan sarakunan gargajiya da suka fito daga yankin da dama dai na cikin mahalarta taron na Kaduna.