✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnonin APC sun ziyarci Wike a Fatakwal

PDP ta sha alwashin za ta rarrashi gwamna Wike ci gaba da zama a cikinta.

Gwamnoni uku na jam’iyyar APC mai mulki a kasar sun ziyarci gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike a gidansa da ke titin Ada George a birnin Fatakwal.

Gwamnonin da suka ziyarci Wike a ranar Juma’a sun hada da Sanwo Olu na Jihar Legas da Oluwarotimi Akeredolu na Jihar Ondo, sai kuma takwaransu na Jihar Ekiti, Dokta Kayode Fayemi.

Babu wani tabbaci dangane da ajandar ziyarar ta su, inda kai tsaye suka shiga ganawar sirri bayan saukarsu a gidan gwamnan na jam’iyyar adawa ta PDP.

Sai dai wasu bayanai na zargin cewa ganawar ba za ta rasa nasaba da kokarin ganin ya fita daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Ana dai ci gaba rade-radin cewa Gwamna Wike na shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC bayan ya sha kaye a hannun tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar a fafutikar neman tikitin takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP.

Kazalika, hakar Wike bata cimma ruwa ba a yunkurin da ya yi na zama abokin takarar Atiku a Babban Zabe na 2023, inda tsohon Mataimakin Shugaban Kasa ya dauki gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takararsa, lamarin da wasu ke ganin shi ya sanya ran Wike ya kara baci.

Sai dai jam’iyyar ta PDP ta sha alwashin rarrashinsa ya ci gaba da zama a cikinta.