✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnonin APC sun nemi El-Rufai ya sasanta da Kungiyar Kwadago

Sun yi gargadi a kan mummunan tasirin da yajin aikin zai yi wa tattalin arzikin Jihar Kaduna.

Gamayyar Gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, sun shawarci takwaransu na Jihar Kaduna, Gwamna Malam Nasir El-Rufai da ya nemi sulhu da Kungiyar Kwadago domin kawo karshen yajin aikin da suka shiga wanda ya gurgunta duk ayyukan tattalin arziki a fadin Jihar.

Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa, Kungiyar ta yi wannan kira ne a yau Talata cikin wata sanarwar ta bakin Shugabanta, Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na Jihar Kebbi.

Gwamna Bagudu ya yi wannan kira tare da gargadin Gwamna El-Rufai a kan mummunan tasirin da yajin aikin zai yi wa tattalin arzikin Jihar Kaduna.

“Kungiyar Progressive Governors (PGF) tana cikin sani tare da damuwa a kan ababen da ke faruwa tsakanin Kungiyar Kwadago NLC da Gwamnatin Jihar Kaduna game da rage yawan Ma’aikatan Kananan Hukumomi.

“Duba da irin kalubalen da ke gaban Jihohinmu, musamman yadda kudin shiga yay i karanci, muna rokon ’yan Najeriya har da NLC da su tattauna da Gwamnatoci a kowane mataki domin kawo karshen wannan matsalar.

“A matsayinmu na gwamnonin APC, muna goyon bayan Gwamnatin Kaduna wajen gyara tsarin Ma’aikatan Kananan Hukumomi domin su yi aiki yadda ya kamata.

“Haka kuma a lokaci guda, muna kira ga Gwamnatin Kaduna karkashin shugabancin takwaranmu, Malam Nasir El-Rufa da ya bi duk hanyoyin da suka kamata wajen sasanta rikici saboda masalahar al’ummar Jiharsa,” in ji Gwamna Bagudu.

Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar Litinin ce Kungiyar Kwadago ta tsunduma yajin aikin kwanaki biyar domin gargadin Gwamnatin Jihar a wani yunkuri na neman ta sauya hukuncin sallamar dubban ma’aikata da ta yi.