Gwamnonin Najeriya sun bai wa Shugaba Muhammadu Buhari shawarar korar duk wani ma’aikacin da ya zarce shekaru 50 a duniya.
Wannan dai na zuwa ne yayin da Najeriya ke fuskantar karancin kudaden gudanar da ayyuka da kuma biyan albashin ma’aikata, sakamakon matsalolin da suka addabi kasar.
- Labaran Auratayya: Wani hanin ga Allah baiwa ne!
- Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram da wasu mayaka 27 a Borno
Gwamnonin sun kuma bukaci shugaba Buhari ya kara yawan harajin da talakawa ke biya, ciki har da sanya haraji a kan kowanne mutum mai samun naira dubu 30 kowanne wata.
Jaridar Premium Times ce ta bankado wannan shawara da gwamnonin suka gabatar wa shugaban kasa lokacin wani taro da suka gudanar da zummar lalubo hanyar samar wa gwamnati karin kudaden kashewa.
Shawarar gwamnonin ta kuma kunshi aiwatar da rahotan Kwamitin Stephen Oronsaye wanda ya bukaci rufe wasu ma’aikatun gwamnati da basu da tasiri ko kuma wadanda ayyukansu ke cin karo da na wasu ma’aikatu.
Rahotanni sun ce Gwamnatin Tarayya a Najeriya na da ma’aikata dubu 89 ne amma kuma tana kashe naira tiriliyan 4 da biliyan 100 wajen biyan su albashi da alawus alawus kowacce shekara daga cikin kasafin kudin naira tiriliyan 17 da ta ke yi a shekara.