Gwamnonin Najeriya sun bukaci a kara farashin litar man fetur taksanin Naira 380 zuwa Naira 408.5.
Kwamitin da gwamnonin da gwamnonin suka kafa ne ya bayar da shawarar a rahoton da ya mika ga taron Kungiyar Gwamnoni Najeriya (NGF) da ya gudana a ranar Laraba.
- Likitoci sun ba El-Rufai awa 48 ya nemi afuwar ma’aikatan jinyan da ya kora
- ’Yan bindiga sun kai harin farko a garin Batsari
A lokacin taron, Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce, “Me zai sa a bar farashin litar mai a N162? An dama an bar farashin a haka ne saboda a baya Gwamnatin Tarayya da kungiyoyin kwadago sun cimma yarjejeniya a kan hakan.”
“Amma ana bayar da tallafin Naira biliyan 70 zuwa biliyan 210 a kowane wata domin a tsayar da farashin litar man fetur a kan N162.
“Farashin N162 bai kai kudin ba, amma idan aka ci gaba da bayarwa asusun Gwamnatin Tarayya zai yi ta raguwa daga Naira biliyan 50 ko mu tashi babu ko sisi, kuma abin zai faru nan gaba ke nan.”
Kwamitin gwamnonin ya goyi bayan a yi karin farashin man fetur sannan a janye tallafin da gwamnati take bayarwa a kai nan take.